Kudin cizo ya mamaye wata jiha a Amurka

Sai dai an gano kudin cizon ya mamaye Gabashin Amurka.

Kudin cizo ya mamaye wata jiha a Amurka

Kudin cizo a kan hannu

Galibi mutane su kan dauka kukin cizo ya kebanta ne ga kasashen Afirka ko kasashen da ba su ci gaba ba irin namu, sai dai kuma al’amarin ba haka ba ne, domin kuwa an gano ya mamaye Gabashin Amurka.

Mazauna Gundumar Arlington da take Jihar Bajiniya (Virginia) da kudin cizon yake addaba sun ce lokacin da suka fara jin cizon sun dauka cizon sauro ne, bayan sun yi fama da rodi-rodi a jikinsu inda daruruwansu suka rika ganin alamun cizon.

Wata mata mai suna Morgan Dailey ta ce wata rana ta wayi gari tana fama da zugin cizo, inda ta rika tunanin ko cizon sauro ne, amma daga basani sai ta gano ba haka ba ne.

“Wurin cizon ya rika kara girma yana ja, wata rana ina cikin aiki sai na ga ya dada girma,” Daily ta shaida wa kafar labarai ta NBC Washington.

Ta ce sai ta nuna wa mahaifiyarta mai suna Betsy Withycombe wurin cizon, wadda take da iyalai masu yawa don haka babu nau’in cizon da ba ta taba gani ba, amma ba ta gane wanne irin nau’i ne ba.

“Muna da ’ya’ya biyar. Na ga nau’o’in cizon kwari iri-iri,” inji Withycombe, wadda ta qara da cewa: “Amma wannan ya sha bamban da wadanda na saba gani a baya.”

A kokarinta na neman bayani, Withycombe ta bi dukkan hanyoyin da suka kamata musamman a Intanet.

Kuma ta sanya bayanai a shafin Facebook tana neman sanin ko wani ya tava ganin irin wannan nau’in cizo.

Nan take sama da mutum 150 suka mayar da jawabi, inda daya daga cikinsu wato Michele Donner, wadda ta ce ita ma tana fama da cizon irin wannan kwaron.

“Yana da matukar kaikayi a ranar farko, sannan sai ya daina. Sannan kowace rana sai cizon ya rika qaruwa,” inji ta.

Ganin matsalar tana ci gaba da karuwa sai Sashin Lafiya na Gundumar Arlington ya ce ba shi da masaniya kan cizon kwaron da mutanen yankin suke fama da shi.

Haka asibitoci masu zaman kansu ba su gano abin da yake faruwa ba.

Daga farko masana sun yi zargin wasu kwari ne dangogin gyare suke addabar mutanen yankin, kamar yadda Kurt Larrick na Sashin Kula da Jama’a na Gundumar Arlington ya shaida wa kafa labarai ta 7News.

Sai dai wadansu kwararru sun nuna shakku a kan haka.

Wani masanin kwari mai suna Dokta Doug Pfeiffer, wanda Farfesa ne a Kwalejin Kimiyya ta Virginia Tech ya ce bai yarda da zargin cewa kwarin dangogin gyare ne suke yin wannan cizo ba.

“Ba na tunanin irin su gyare da dangoginsa ne suke cizon,” inji Pfeiffer.

A karshe bayan dogon bincike, likitoci sun gano cewa kudin cizo ne yake addabar mutanen, inda suka shawarci mutanen yankin da su dauki matakan kare kansu.

Haka kuma sun bukaci mutanen yankin da su rika feshin maganin kwari sannan su tsabtace muhallansu tare da rika tuntubar asibitoci a duk lokacin da suka hadu da cizon.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja