Kudin da ka ba ni sun yi yawa – Dan fashi ga ma’aikacin banki
…Ka ba ni fiye da kudina Jami’an ’yan sanda na tuhumar wani mai suna Sandy Hawkins a birnin Boca Raton da ke jihar Florida ta Amurka, saboda zargin yin fashi a banki duk da babu makami a hannunsa. Boca mai shekara 73, ya bukaci wani ma’aikacin banki ne ya bashi Dalar Amurka 1,100 (daidai da […]
…Ka ba ni fiye da kudina
Jami’an ’yan sanda na tuhumar wani mai suna Sandy Hawkins a birnin Boca Raton da ke jihar Florida ta Amurka, saboda zargin yin fashi a banki duk da babu makami a hannunsa.
Boca mai shekara 73, ya bukaci wani ma’aikacin banki ne ya bashi Dalar Amurka 1,100 (daidai da Naira dubu 399) . Da ma’akacin bankin ya kirga Dala 2,000 (daidai da Naira dubu 725) ya mika masa sai Sandy ya ce, “Haba duk da furfurata a ce zan yi cuta?”
A tsarin bankin sun binciki Sandy ne saboda nuna son kudinsa a fili da ya yi a reshen bankin Walls Fargo da ke Boca Raton ta Yamma. Hakan ya sa jami’an tsaro suka rike Sandy, suna tuhumarsa a matsayin wanda ya shiga bankin don yin fashi.
Wani tsohon ma’aikaci da ya yi ritaya ne ya yi sanadiyyar kama Sandy, kamar yadda rahoton ya tabbatar daga bisani ofishin jami’an tsaro na Palm Beach suka fara bincike.
Rahoton ya ce, Sandy, ya ciro wasu tsofaffin takardun ajiyar kudi daga cikin aljihunsa, a jikin bayan takardun an rubuta, “Ku ba ni Dalar Amurka 1,100 yanzu,” ba tare da fargabar za a iya kama shi ba.
Rayuwar Sandy ta canja ce daga watan Satumban 2013, bayan rasuwar matarsa Linda a 1997 sanadiyyar cutar amosalin jinin da ta yi ajalinta.
Wani wanda Sandy, ya taba zama a gidansa mai suna Scott Bail, ya ce ya yi matukar sanin Sandy, ya nada kyakkyawar alaka da mutane.
Scott, ya ce abu ne mai matukar mamaki Sandy ya sauya dabi’unsa a iya saninsa da ya yi lokacin da yake haya a gidansa. Sandy tsohon ma’aikaci ne a kamfanin da ke kera na’urar sanyaya daki sannan uwargidansa matuniyar kirki ce.
Scott Bail, ya ce bai yi magana da Sandy ba tun lokacin da ya sayar da gidan da Sandy ya zauna bayan mutuwar matarsa, sannan wanda ya sayi gidan ya ce zai ci gaba da bai wa Sandy hayar gidan da yake zaune. A ranar Talata da wuce da yamma aka yankewa Sandy hukuncin zaman gidan yarin Karamar Hukumar Palm Beach, inda ake tuhumrsa da laifin fashin kudi ba makami.
Alkalin kotun Palm Beach mai suna Ted Booras, ya yanke wannan hukuncin ne tare da tarar biyan kudin da ya kai dalar Amurka $50,000 daidai da Naira miliyan 18. Lauyan da yake kare Sandy a kotun mai suna Paul Caruso, ya ce ba a taba kama Sandy a tarihi da laifin wani abu ba, sannan shi tsohon ma’aikaci ne da ya yi ritaya kuma shi dan asalin garin Detroit da ke jihar Michigan ta Amurka, amma duk ba a bayyana tarihinsa ba a kotun wajen yadda dabi’unsa suke.
Kotun Palm Beach, ba tada wani rahoto da yake nuna cewa an taba kama Sandy da laifi, an dai ta kiran wayar salurar Sandy ba adadi saboda rashin ganinsa. Kamar yadda rahoton ya sanar.
A cewar rahoton a ranar Litinin lokacin da kowa yake cikin aiki sai ga wani mutum ya shigo sashen da ake karbar kudi sanye da tabarau a reshen bankin Sandalfoot, Karamar Hukumar Broward.
Ma’aikacin da yake bada kudin ya ce, mai fashin kudin ya tambaya a bashi kudi Dalar Amurka $1,100, amma da mai bada kudin ya tambaye shi ina katin cire kudinsa, sai Sandy ya mayar da martani akan cewa ai wannan fashi ne, “Ina da makami ai.” Bayan Sandy ya saka hannunsa a cikin aljihu sai gashi ya curo kudin da ya kai dalar Amurka $2,000, amma duk da haka ya dage sai an ba shi kudi dalar Amurka dubu $1,100. An gano rashin gaskiyar da Sandy ya shirya ne ta hanyar amfani da na’urar daukan hoton bidiyo na cikin bankin da ke daukar harkokin kasuwancin da yake gudana a harabar.
Bayan duk tabbatar da wadannan hujjojin nadar hotunansa a matsayin wanda ya yi fashin banki sai jami’an tsaro su kaje har gida suka kama shi don tuhumarsa.