Kudin gudanarwa: Shehu Sani ya kwanto wa sanatoci kura
Majalisar Dattawa ta tabbatar da cewa kowane Sanata yana karbar Naira miliyan 13 da rabi a matsayin kudin gudanarwarsa da albashi duk wata. Majalisar ta bayyana haka jim kadan bayan daya daga cikin ’yan majalisar, Sanata Shehu Sani ya shaida wa jaridar Daily Trust wata cewa kowannensu yana karbar Naira miliyan 13 da rabi a […]

Majalisar Dattawa ta tabbatar da cewa kowane Sanata yana karbar Naira miliyan 13 da rabi a matsayin kudin gudanarwarsa da albashi duk wata. Majalisar ta bayyana haka jim kadan bayan daya daga cikin ’yan majalisar, Sanata Shehu Sani ya shaida wa jaridar Daily Trust wata cewa kowannensu yana karbar Naira miliyan 13 da rabi a matsayin kudin gudanarwa da albashi duk wata.
A cewar Sanata Shehu Sani, “Baya ga haka kowane Sanata yana karbar Naira dubu 700 a matsayin albashinsa na wata ban da sauran alawus-alawus da ake ba mu.”
Sanata Shehu Sani ya ce bai yi wannan tonon silili da manufar tozarta majalisar ba, illa dai saboda kallon da wadansu ke yi musu na barayi marasa gaskiya masu boye abin da suke samu.
Ya kara da cewa sama da shekara 19 ke nan da ake zargin ’yan majalisa na karbar miliyoyin Naira amma kuma sun kasa fitowa su kare kansu, su yi wa ’yan Najeriya bayanin ainihin kudaden da suke dauka a matsayin albashi ko na alawus-alawus.
Sannan ya ce ya yi maganar ce don sauran bangarorin gwamnati da suka hada da alkalai da ministoci da gwamnoni da duk wadanda suke rike da madafun iko su bayyana wa jama’a adadin kudin da suke samu da kuma abin da suke yi da su.
Wannan tonon silili da Sanata Shehu Sani ya yi wa ’yan uwansa Sanatoci ne, ya sa Kakakin Majalisar Dattawa, Sanata Sahabi Ya’u fitar da sanarwar da ke tabbatar da kalaman takwaran nasa.
Ya ce Sanata Shehu Sani bai fadi wani sabon abu ba game da albashi da sauran kudin gudanar da aikin dan majalisar ba, saboda da ma wadannan bayanai suna cikin kasafin kudin Majalisar Dokoki ta kasa, wanda kuma kowa ya sani, in ji sanarwar da Sanata Ya’u ya fitar.
Sanarwar da ya fitar ta zo ne sakamakon sukar da ’yan majalisar ke sha a wurin ’yan Najeriya wadanda ke ganin ’yan majalisar na karbar makudan kudi amma sun kasa tsinana wa al’ummar da suke wakilta komai.
A baya dai an sha yin kira ga ’yan majalisar su bayyana albashi da sauran kudaden da suke karba. Wannan lamari yana faruwa ne a lokacin da ’yan Najeriya ke fama da matsanancin talauci sakamakon tashin farashin kayan masarufi da tsadar rayuwa.