Kudin gyaran majalisa zai iya gina kananan asibitoci 27,000
A farkon makon nan ne aka samu labarin amincewa da kasafin Naira biliyan 37 da aka amince wa Majalisar Dokoki ta Kasa domin gyaran majalisar. Mutane da dama sun nuna takaici kan lamarin, inda wadansu ke ganin ba laifi.. Wannan kudin yana cikin kasafin kudin badi da Shugaban Buhari ya rattaba wa hannu. Bincike ya […]
A farkon makon nan ne aka samu labarin amincewa da kasafin Naira biliyan 37 da aka amince wa Majalisar Dokoki ta Kasa domin gyaran majalisar.
Mutane da dama sun nuna takaici kan lamarin, inda wadansu ke ganin ba laifi..
Wannan kudin yana cikin kasafin kudin badi da Shugaban Buhari ya rattaba wa hannu.
Bincike ya nuna cewa an gina majalisar ce a kan Naira biliyan 10.7 a 1996, wanda ke nuna kudin da aka kasafta don gyarar ya kai ukun wanda aka gina ta.
Wani nazari da Aminiya ta yi, Naira biliyan 27 za ta gina kananan asibitoci (PHC) 27,000 a fadin kasar nan.
Wani jami’in lafiya, Dokta Ifeanyi Cajetan Casmir ya ce Naira miliyan 10 za ta iya gina Asibitin PHC daya, wanda aka lissafa, zai kama asibitin PHC 27,000 ke nan a kan kudi Naira biliyan 37.