Karyewar FTX: Gwamnati ta a kwace kadarorin kamfanin

Masu hannayen jari a FTX na neman diyyar Dala biliyan 11 daga kamfanin da ya samu karayar arziki

Karyewar FTX: Gwamnati ta a kwace kadarorin kamfanin

A makon jiya FTX ya sanar cewa ya samu karayar arziki. (Hoto: Marco Bello/Reuters)

Hukumar Hadahadar Hannayen Jari ta Kasar Bahamas ta kwace kadarorin kamfanin kudaden intanet na FTX wanda ya samu karayar arziki cikin mako guda.

A ranar Alhamis Hukumar ta kwace kadarorin FTX da asusun ajiyar kamfanin ta mika shi ga wani kamfanin kula da kudade ta intanet (FDM) domin adana.

Hukumar ta ce, “Daukar wannan matakin gaggawa ya zama dole domin kare dukiyoyin masu hannayen jari da sauran abokan huldar FTX.”

Karyewar FTX wanda shi ne kudin intanet na uku mafi karfi a duniya ya girgiza bangaren tare da haifar da zargin masu shi da zambatar masu zuba jari.

A halin yanzu masu hannayen jari a FTX sun shigar da karar neman Dala biliyan 11 daga mai FTX, Sam Backman-fried da sauran jagororin kamfanin.

A bangare guda kuma hukumomin kasar Amurka na bincikar masu kamfanin kan zargin saba dokokin Hada-hadar Kudade da Hannayen Jari.

A makon jiya ne FTX ya sanar cewa ya samu karayar arziki bayan masu hannayen jari sun janye Dala biliyan shida cikin dan kankanin lokaci.

Duk da kokarin farfado da shi da takwaransa, Binance, ya yi, amma abin ya  gagara.