Kudin litar man jirgi ya karu zuwa N400

Kamfanonin sufurin jiragen sama na shirin kara kudi saboda tashin farashin mansu zuwa N400

Kudin litar man jirgi ya karu zuwa N400

Masu gidajen mai da kamfanonin jiragen sama sun shiga damuwa a sakamakon tashin farashin litar man jirgin zuwa N400.

A yayin da farashin man ya yi tasin gwauron zabo, kamfanonin sufurin jiragen sama na shirin kara farashi, ganin yadda tsadar man ke barazana ga harkokinsu.
Binciken da Aminiya ta gudanar a ranar Laraba ya gano ana sayar da litar man jirgi a kan N407 a Kano, amma a Abuja, Inugu da Fatakwal da Uyo ana sayarwa N395, Legas kuma N375.

Kafin nan, farashin man jirgi N310 zuwa 330 ne a watan Nuwamban 2021, gwarwadon wurin da ake sayarwa.

Tashin farashin zuwa N400 na nufin karin kashi 233 ciki 100 ke nan aka farashin, idan aka kwatanta da Naira 120 da ake sayarwa a shekara shida da suka gabata a Najeriya.

A shekarar da ta gabata ne aka yi hasashen cewa farashin man jiragen saman zai kai N400, kuma an ga hakan a makon da ya gabata.

Idan za a iya tunawa farashin man jirgi bai wuci N120 zuwa N160 ba a shekarar 2006.

Karin kudin jirgi

Tashin gwauron zabon da farshin ya yi ya sanya fargabar tashin kudin jirgi, a yayin da majiyoyi ke cewa kamfanonin jirgin sama na shirin kara farashin tikitinsu.

Majiyoyin sun ce akwai yiwuwar nan ba da jimawa ba kamfanonin jirgin sama za su kara farashinsu, “Daidai da tashin gwauron zabon da man jirage ya yi, wanda kuma ke barazana ga dorewar kamfanonin sufurin jiragen sama.”

Dillalan man fetur sun shaida mana tashin Dala da rashin tallafin gwamnati ne suka haddasa tashin gwauron zabon da aka samu.

Wani dillalin man jirage ya shaida wa wakilinmu cewa, “Gwamnati ta cire hannunta a harkar man jirage. Idan ka duba, yanzu nawa Dala take? Kai da kanka ka lissafa ka gani. Abu ne a fili, babu wani boye-boye.”

A halin yanzu dai ana shigo da man jirgi zuwa Najeriya ne daga kasashen waje, a yayin da farashin Dala yake N415 a gwamnatance, a kasuwar bayan fage kuma ake sayar da ita a kan N570.