Kudin marayu ya kara makalewa a kotun Kaduna ..Saura qiris ya fado

Kimanin shekaru biyu ke nan da rasuwar wani fitaccen dan kasuwa da ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a PZ da ke Zariya, watau marigayi Alhaji Yahaya Rawun mutumin Kwanar dangora cikin Jihar Kano, sai dai har yanzu iyalansa ba su samu damar raba gadon dukiyar da mahaifin nasu ya rasu ya bari ba, sakamakon batan […]

Kudin marayu ya kara makalewa a kotun Kaduna ..Saura qiris ya fado

Kimanin shekaru biyu ke nan da rasuwar wani fitaccen dan kasuwa da ke gudanar da harkokin kasuwancinsa a PZ da ke Zariya, watau marigayi Alhaji Yahaya Rawun mutumin Kwanar dangora cikin Jihar Kano, sai dai har yanzu iyalansa ba su samu damar raba gadon dukiyar da mahaifin nasu ya rasu ya bari ba, sakamakon batan dabo da kudin da ya bari suka yi a wata kotun Shari’ar Musulunci a jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan rasuwar marigayin sai iyalansa, wadanda suka hada da matansa na aure biyu da ‘ya’yansa 17 da kuma mahaifiyarsa, suka gayyaci Alkali Mahmud Shehu da ke kotun Shari’ar Musulunci da ke Kawo a Jihar Kaduna don ya raba musu gado. Sai dai kasancewar dukiyar da marigayin mahaifin nasu ya bari suna wani banki sai hukumar bankin ta ce sai an kawo takardar kotu (Court order), inda daga nan ne wancan kudi da marigayin ya bari, da yawansu ya kai Niara miliyan 22 suka fada asusun kotun da wannan Alkalin yake aiki.
Sai dai kuma fitowar kudin daga asusun kotun sai ta gagara, domin kamar yadda iyalan marigayin suka nuna, kotun ta sanya wa iyalan mamacin sharadin sai sun cire kashi goma na adadin kudin wanda za su fada aljihun Alkalin alkalai (Grand Khadi) na Jihar Kaduna kafin akai ga raba musu kudin, sharadin da iyalan suka ki amincewa da shi.
Alhaji Abubakar Yahaya daya ne daga cikin ‘ya’yan marigayin, ya shaida wa Aminiya cewa, “Tun daga wancan lokaci da muka ki yarda mu biya wanan kashi 10 da Alkali Mahmud Shehu ya gaya mana cewa za a bayar da shi ga Grand Khadi na Jihar kaduna sai aka ki fito mana da kudinmu, inda aka rika daga mana lokac,i a ce yau, a ce gobe, har muka gaji muka daina bin maganar. Koyaushe muka je kotun babu wata kwakwarar magana da za a gaya mana, sai a karshe aka ce wai wata rajistarar kotun mai suna Lami Kwasau ta kwashe kudin ta gudu, don haka sai dai mu bayar da wadansu kudi masu kauri da za a yi amfani da su wajen nemanta. A nan ma dai muka ki amincewa da wanan batu.To sai daga baya ne muka shigar da kara kotu, inda muka yi karar Alkali Mahmud Shehu da nufin a karba mana hakkinmu da ya makale a wuirnsa. A nan ma dai haka aka yi ta daga shari’ar har zuwa wannan lokaci da muke ciki kudin ba su kai ga fitowa ba. Bayan ga karar da muka shigar kotu, mun shigar da makamancita, wato korafi ga Hukumar Yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa tu’annati (EFCC).” Inji shi.
Game da jita-jitar da ake yadawa cewa gwamnatin Jihar Kaduna ta yi alkawarin biyan marayun kudinsu kuwa, sai ya ce, “Da muka gaji da halin da muke ciki sai muka shiga gidan rediyo muka fadi halin da muke ciki. lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna Ramalan Yero ya ji halin da muke ciki sai ya umarci Ma’aikatar Shari’a da ta biya mu kudinmu. To amma a zama biyu da muka yi da Kwamishinan Shari’a ya bayyana mana cewa ma’aikatar tasu a wannan lokaci ba ta da kudin da za ta biya mu, sai dai mu jira har sai ta nemi kudi daga wurin Gwamna sanann za ta neme mu.” Inji shi.
Alhaji Abubakar ya kara da cewa,”A haka muka zauna har sai a karshen watan Disambar nan sanann suka kira mu suka ce kudinmu sun fito za a ba mu, amma da sharadin sai mun janye karar da muka shigar gaban kotu da kuma wacce muka shigar gaban Hukumar EFCC. A yanzu dai mun yi magana da lauyanmu inda zai hadu da lauyan gwamnati don janye wadancan kararraki da muka shigar.” Inji shi.
Aminiya ta tuntubi Alhaji Sani wanda shi ne wakilin kuma babban aminin marigayin, inda ya tabbatar da cewa an fada musu cewa gwamnati ta bayar da kudin domin a biya iyalan marigayin, amma sai dai har yanzu ba su samu wannan kudi ba.
Ya ce a ranar Asabar din nan da ta wuce sun zauna da tsoho da sabon alkalin alkalai Ggrand khadi) na jahar da kuma marayun marigayi. ‘’An nan ne suka sanar da mu cewa gwamnati ta bayar da wannan kudi domin a biya marayun, amma wai sai dai ta hannun lauyoyinmu.’’
“ Abin da na sani shi ne, lauyarmu ya ba lauyan gwamnati takarda kamar yadda suka bukaci mu yi. Kuma sun ce idan muka yi haka za a biya wannan kudi a ranar litinin ko talatar nan da suka wuce, amma zancen da nake da kai a yanzu ba ni da masaniyar ko an biya, domin na kira lauyanmu inji inda aka tsaya amma bai dauki wayata ba, saboda kila suna cikin taro. Yanzu dai halin da ake ciki ke nan, da zarar an samu bayani zan sanar da kai,” inji shi.