Kudin na’urar kayyade gudu ya yi yawa – Alhaji Salihu
A ‘yan kwanakin nan ne Hukumar kare hadura ta kasa ta sanar da yin amfani da na’urar kayyade gudu a motocin haya, a kasar nan baki daya. Wakilinmu ya tattauna da shugaban kungiyar masu motocin sufuri (NURTW) a Jihar Nasarawa, Alhaji Salihu Adamu game da batun. Ya kuma tabo batun rigimar da ta auku […]
A ‘yan kwanakin nan ne Hukumar kare hadura ta kasa ta sanar da yin amfani da na’urar kayyade gudu a motocin haya, a kasar nan baki daya. Wakilinmu ya tattauna da shugaban kungiyar masu motocin sufuri (NURTW) a Jihar Nasarawa, Alhaji Salihu Adamu game da batun. Ya kuma tabo batun rigimar da ta auku tsakanin ’ya’yan kungiyarsa da na takwararta NARTO a jihar kwanan nan da sauran batuttuwa. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Mene ne ra’ayinka game da na’urar kayyade gudu da Hukumar kare hadura ta umurci mambobinku su yi amfani da ita?
Alhaji Salihu: Ni dai zan iya cewa kirkiro da na’urar ta dace sosai don ba shakka zai rage guje-guje da wasu direbobinmu ke yi fiye da ka’ida. Amma a wani bangaren kuma zan ce bana goyon bayan yin amfani da na’urar, musamman idan aka yi la’akari da yadda aka sa mata kudi da yawa, wato Naira dubu 45. Ka ga yanzu ana fama da tsadar rayuwa, kuma ba kudi harkoki ba sa tafiya kamar yadda aka saba. Kuma sau da yawa za ka ga farashin kayayyaki sun karu, amma ban da kudin shiga mota don idan direbobi suka ce za su kara kudin shiga mota fasinjoji ba za su yarda ba. A haka sai a zo a ce su sayi wannan na’ura da tsada har Naira dubu 45. Ka ga ba a yi wa direba adalci ba idan aka yi haka. Saboda haka abin da nike nufi a nan, shi ne a wani bangaren ina goyon bayan kirkiro da wannan na’ura a wani bangaren kuma ba na goyon bayan haka, don kudin sayanta ya yi wa direbobi yawa, musamman a wannan lokaci da ake fama da rashi. Ka ji korafi da direbobi ke yi ke nan tun da aka sanar da yin amfani da na’urar. Kuma ina so inyi amfani da wannan damar in yi kira ga hukumar kare hadura da gwamnatin tarayya, ta sake dubawa, ta rage kudin na’urar zuwa Naira 2000 ko a kalla ka da ya wuce dubu biyar (5000), don bai wa direbobinmu damar malakarta don amfanin kansu.
Aminiya: Hakumar kare hadurra ta bayyana cewa masu motocin kansu (pribate) ba za su yi amfani da na’urar ba sai masu motocin haya, ya kake gani?
Alhaji Salihu: To da farko dai zan ce wannan batu cewa, masu motocin haya ne ke hadasa hadura a hanya ba gaskiya ba ne. Don idan ka lura galibin hadurra da ke faruwa a hanyoyinmu sukan auku ne tsakanin motocinmu na fasinja da na masu zaman kansu. Da wuya ka ga motoci biyu sun yi hadari kuma dukansu na haya ne. Ba ina cewa hakan ba ya faruwa ba, amma da wuya. Na tabbata cewa abin da ya sa ka ji ana wannan zargi, shi ne, kasancewar motar haya ta fi kwasar mutane da yawa fiye da na masu zaman kansu (pribate). Shi ya sa idan hadari ya auku a kan rasa rayuka da dama fiye da na ‘pribate,’ don shi ‘pribate’ mutane da yake kwasa ba su da yawa, a wasu lokuta ma za ka tarar idan hadari ya auku shi kadai ne a mota. Shi ya sa a ke ganin kamar motocinmu ne, wato na sufuri ko in ce na haya ne kadai ke jawo hadura a hanya. Kuma kada ka manta akwai masu motocin kansu da dama da suke gudun fitar hankali, wasu ma sai sun sha kayan maye suke tuki. Idan sun hau hanya sai ka ga suna jawo hadurra ana rasa rayuka. Saboda haka su ma ya kamata a tilasta musu sayen wannan na’ura don galibinsu suna jawo hadurra sau da yawa kamar yadda na bayyana.
Aminiya: Me ya sa ake samun sabani tsakanin ‘yan kungiyarku da ta takwararku ta NARTO?
Ba shakka sau da yawa mukan samu sabani tsakaninmu da su. Kuma babban musabbabin rigirgimun shi ne shiga aikinmu da suke yi sau da yawa. Kamar yadda ka sani akwai bambanci a ayyukanmu da nasu. Wato NARTO kungiya ce ta masu manyan motoci da suke bayarwa ake haya da su a kasar nan. Mu kuma kungiyarmu ta masu motocin haya ne. Kodayake mambobin NARTO suna zaman iyayen gidanmu ne, don suna da motocin haya. Amma maimakon kowa ya tsaya a matsayinsa, ko in ce a aikinsa sai ya kasance suna shigar mana aiki, inda wasu ke sayar da rasiti, wato aikin da muke da dama da izinin yin haka, kuma suna yi ba bisa ka’ida ba. Suna kuma lodi a garejinmu ba tare da sun bi dokar garejin ba, da dai sauran ayyuka da ya kamata mambobinmu su yi. Shi ya sa a ‘yan kwanankin nan ma kamar yadda ka sani sai da aka samu rashin jituwa tsakanin wasu mambobinmu da nasu, a wasu garuruwa da ke shiyyar Nasarawa ta Kudu da suka hada da Keffi da Nasarawa da Toto da sauransu, inda ba don jami’an tsaro da kuma taimakon Allah ba, da an samu babbar matsala sakamakon tarzomar. Amma mun gode Allah a karshe mun shawo kan lamarin, kuma kura ta lafa a halin yanzu.
Aminiya: Wane mataki shugabanni ke dauka wajen hada kan ’ya’yan kungiyoyinku?
Alhaji Salihu: A bangarenmu na shugabanni dai sau da yawa mukan gudanar da tarurruka ne tare da shugabanninsu, wato NARTO don abin da na zo na tarar ana yi a nan ke nan. Wato na zo na tarar da kyakkyawar dangantaka ne tsakanin kungiyarmu da ta su, inda har yanzu mukan ja hankalin mambobinmu baki daya su zauna lafiya, kowa yasan iyakarsa a sana’armu. Mukan kuma gaya wa ‘yan kungiyarsu cewa, idan suna sha’awar aikinmu ne a shirye muke mu karbesu muddin sun zo mun yi musu rajista, sannan su kama aiki. Kuma ina so in sanar da kai cewa a halin yanzu mambobinsu sama da 130 sun dawo kungiyarmu, inda bayan mun yi musu rajista muna kuma aiki tare da su.