Kudin shigar simintin Dangote ya kai Naira biliyan 805 a shekarar 2017
Kamfanin siminti na Dangote jiya ya fitar da harkokin kudin kamfanin na shekarar 2017 wanda ya nuna karuwar cinikin kamfanin daga Naira biliyan 615 a shekarar 2016 zuwa Naira biliyan 805 a shekarar 2017. Ribar da kamfanin ya ci kafin haraji ya karu daga Naira biliyan 180 a shekarar 2016 zuwa Naira biliyan […]
Kamfanin siminti na Dangote jiya ya fitar da harkokin kudin kamfanin na shekarar 2017 wanda ya nuna karuwar cinikin kamfanin daga Naira biliyan 615 a shekarar 2016 zuwa Naira biliyan 805 a shekarar 2017.
Ribar da kamfanin ya ci kafin haraji ya karu daga Naira biliyan 180 a shekarar 2016 zuwa Naira biliyan 289 a shekarar 2017 sannan kuma riba bayan fitar da haraji kamfanin ya samu Naira biliyan 142 a shekarar 2016 zuwa Naira biliyan 204 a shekarar 2017.
Kamfanin ya gabatar da rabon ribar Naira 10 da digo 50 a kowane hannun jari.
Rahoton ya nuna cewa cinikin da aka samu daga inda ake sarrafa simintin da ke Najeriya su ne suka sanya kamfanin ya samu Naira biliyan 552