Kudin sufuri ya karu saboda wahalar man fetur a Sakkwato

Na sayi galan daya kan N2000, sufuri ya yi tsada duk in da za ka je sai ka ninka kudi.

Kudin sufuri ya karu saboda wahalar man fetur a Sakkwato

Yadda ababen hawa ke bin layin shan man fetur a Abuja

Matsalar karancin man fetur da ake fama da ita a Najriya, a Jihar Sakkwato abin ya ta’azara inda al’umma suka shiga halin ni ’ya-su musamman a fannin harkokin sufuri wanda kudin da ake daukar jama’a zuwa unguwannin a ciki da wajen gari ya ninku.

A zantawar da Aminiya ta yi da wasu mazauna jihar, sun bayyana cewa karancin man fetur ya jefa su cikin halin kakanikayi matuka, la’akari da karancin kudi a hannun jama’a wanda ya sa rayuwar ta kara kunci.

Bashar Danfari ya ce ana jin jiki sosai a wannan karancin man fetur a Jihar Sakkwato, “da wannan safiyar ta yau na zagaya ko’ina a cikin gari gidajen mai a rufe bayan gida biyu da na gani a bude suna sayarwa kan naira 205 duk litar.

“Su ma gidajen man da suka bayarwa akwai zungura-zunguran layika da sun wace a buga misali don akwai wanda ko zai samu man sai ya kai maraice in har gidan man bai rufe ba,”a cewar Danfari

Ya ce “a nan Sakkwato ’yar karamar jarkar da muke saye naira 80 ta koma 200, wadda muke saye 200 ta koma 400, ta 400 ta koma 700, galan guda kuma 1900 zuwa 2000, a haka ake ta wahalar.”

Abubakar Taraliya mai sana’ar Acaba ya ce mai ya yi wahala a wurin ’yan bunburutu, “don na sayi mai galan daya kan naira 1500 don haka duk wanda nake daukar mutum ya biya naira 70 yanzu sai 150 saboda tsadar da man fetur din yayi.”

Shi ma wani Yusuf Muhammad ya koka kan yadda wahalar man ke kawo masu matsala ga walwalarsu, inda ya ce “ya sayi galan daya kan naira 2000, sufuri ya yi tsada duk in da za ka je sai ka ninka kudi, ababen hawan ma sun yi karanci a gari.”