Kudin tashar Mambilla: An ba da belin tsohon ministan lantarki kan N10bn

Ana zargin Saleh Mamman da wawure kadaden aikin tashoshin wutar lantarki na Mambilla da na Zungeru

Kudin tashar Mambilla: An ba da belin tsohon ministan lantarki kan N10bn

Babbar Kotun da ke Abuja ta ba da belin tsohon ministan lantarki, Injinia Saleh Mamman a kan kudi Naira biliyan 10 da mutane biyu da za su tsaya masa.

An gurfanar da Saleh Mamman ne bisa zargin da ake masa da wawure Naira biliyan 33 daga kadaden aikin katafarun tashoshin wutar lantarki na Mambilla da na Zungeru.

Mai Shari’a James Omotosho ya ce idan tsohon ministan ba shi da Naira biliyan 10 na belin da ko kotun ta nema, zai iya karbar lamuni ko yarjejeniya da banki.

Alkalin kotun ya kuma shardanta masa kawo mutum biyu wanda kowannensu zai ajiye Naira miliyan 750 su tsaya masa.

Dole ne kuma su mallaki gine-gine a Abuja kuma su kawo takardun shaidar biyan haraji na shekaru uku a jere da kuma hotunansu.

Shi kuma Saleh Mamman zai damka wa kotun takardar fasfo dinsa na fita kasar waje.

Daga nan Mai Shari’a Omotoshoya ba da umarnin a ci gaba da tsare tsohon ministan a gidan yarin Kuje, har sai ya cike sharuddan belin.

An dage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Satumba.

Kotun ta ba da umarnin tsare tsohon ministan a gidan tari ne bayan hukumar EFCC ta gurfanar da shi kan badakalar Naira biliyan 33.

Tun a ranar Alhamis alkalin ya ba da umarnin kai wanda ake zargin kurkuku ba ya musa laifuka 12 da hukumar EFCC ke zargin sa da aikatawa a lokacin da yake kan kujerar minista a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ana zargin Saleh Mamman da amfani da wasu jami’an ma’aikatarsa wajen karkatar da kudaden aikin tashoshin lantarki na Mambilla da Zungeru.

EFCC ta ce a lokacin da take gudanar da bincike ta gano wasu kadarori masu alaka da tsohon ministan a ciki da wajen Najeriya, baya ga tsabar makudan kudade.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos