Kudu za ta koya wa Arewa hankali a zaben 2015 idan… – Osoba

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun kuma jigo a Jam’iyyar APC da ake rade-radin zai koma PDP Aremo Segun Osoba ya yi barazanar cewa a zaben 2015, Kudu za ta koya wa Arewa hankali idan Arewar ta ki canja tafiya kan batun mallakar albarkatun maid a ake takaddama a wurin taron kasa da sauran batutuwa.Batun mallakar albarkatun […]

Kudu za ta koya wa Arewa hankali a zaben 2015 idan… – Osoba
Kudu za ta koya wa Arewa hankali a zaben 2015 idan… – Osoba

Tsohon Gwamnan Jihar Ogun kuma jigo a Jam’iyyar APC da ake rade-radin zai koma PDP Aremo Segun Osoba ya yi barazanar cewa a zaben 2015, Kudu za ta koya wa Arewa hankali idan Arewar ta ki canja tafiya kan batun mallakar albarkatun maid a ake takaddama a wurin taron kasa da sauran batutuwa.
Batun mallakar albarkatun kasa na daya daga cikin batutuwan da ake takaddama kansu a taron kasa da ake gudanarwa a halin yanzu inda mutanen yankin Kudu maso Kudu suke bukatar a kara kudin da ake ba su daga albarkatun man fetur zuwa kashi 25 maimakon kashi 13 cikin 100 a yanzu.
Wakilan Kudu maso Gabas da na Kudu maso Yamma sun goyi bayan a kara musu zuwa kashi 21 da digo 5, yayin da wakilan Arewa suke adawa da duk wani batun kari, suna bukatar a ci gaba da bin tsarin da ake kai a yanzu.
Osoba wanda ke tofa albarkacin bakinsa kan rahoton Kwamitin Rarraba Iko na taron ya ba wakilan mamaki, lokacin da ya yi gargadin cewa idan Arewa ba ta sauya matsayi a yanzu ba, Kudu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin ramako a zaben 2015 ba.
Cif Osoba ya soki wakilan Arewa da rashin nuna damuwa da matsalolin ’yan Najeriya da suke fama da illar da hakar man fetur ke haifar musu.  
Shi kuwa tsohon Gwamnan Jihar Oyo Sanata Rashid Adewolu Ladoja, ya koka ne kan yadda wakilan taron suke barazana ga juna domin cimma wasu bukatunsu, inda ya yi kira su guji musguna wa juna.
Ladoja wanda ke mayar da martani kan korafin da wani wakili daga Kudu maso Gabas ya yi cewa ana tauye su a kasar nan, ya ce: “Suna da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya da Ministar Kudi da Sakataren Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Babban Banki da sauransu. Don haka a kan me kuke magana? Abin da muke cewa shi ne dukkanmu ’yan Najeriya ne, Ibo bangare ne na Najeriya kuma ina sonsu.”