Kududdufin mutuwa na Du

Yadda Rundunar Sojin Najeriya ta bankado yadda ake kashe matafiya a jefa su cikin kududdufin Du ya jefa mutane cikin rudani a duk fadin kasar nan. An gano kududdufin ne a garin Dara da ke yankin Du a Karamar Hukumar Jos ta Kudu. Bangaren bincike na sojojin Najeriya ne suka gano kududdufin bayan bacewar wani […]

Kududdufin mutuwa na Du
Kududdufin mutuwa na Du

Yadda Rundunar Sojin Najeriya ta bankado yadda ake kashe matafiya a jefa su cikin kududdufin Du ya jefa mutane cikin rudani a duk fadin kasar nan. An gano kududdufin ne a garin Dara da ke yankin Du a Karamar Hukumar Jos ta Kudu. Bangaren bincike na sojojin Najeriya ne suka gano kududdufin bayan bacewar wani janar mai ritaya.

Manjo Janar Idris Alkali, wanda kwanan nan ya yi ritaya a matsayin Babban Jami’in Mulki na Hedkwatar Sojin Najeriya da ke Abuja, ya bace ne tun ranar 3 ga watan Satumba. Ya bar Abuja ne a motarsa kirar Toyota a kan hanyarsa ta zuwa gonarsa a Bauchi. Karshen lokacin da ya zanta da iyalansa shi ne lokacin da ya kusa shiga Jos, kafin bacewarsa. Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ne ya bayar da umarni ga sashen bincike na Runduna ta 3 da ke Rukuba a Jos da ya binciki lamarin.

Bayan bincike mai zurfi, sai jami’an sojojin suka samu labarin kududdufin. Kuma cikin ikon Allah, kafin a fara binciken kududdufin, sai wadansu mata kimanin 500 sanye da bakaken kaya wadansu kuma ba cikakkun tufafi a jikinsu suka fara zanga-zangar kin amincewa da binciken. Sun rika jifar sojojin har wadansu ma suka yi kokarin kwace makami daga sojojin.

Matan sun ce matsalarsu ita ce yadda sojojin suka yi dafifi a garinsu. Kakakin matan, Mary Yakubu ta ce bai kamata a kwalfe kududdufin ba domin hakan zai jawo bala’i da mace-mace a garin. Ta ce tun zamanin iyaye da kakanni, babu wanda ya taba yin kokarin kwalfe kududdufin. Wannan maganar kanzon korege ce kawai domin kududdufin na mahaka ma’adinai ne, kuma ba zai yiwu ya kai lokacin da take ikirari ba. Bisa la’akari da abin da ya faru, kawai wadansu miyagun maza ne da ke Du din suka yi amfani da matan domin rufe barnar da suke yi.

Abin mamaki kuwa, lokacin da sojojin suka kwalfe kududdufin, sai suka gano motar janar din da ya bace da wasu kayayyakinsa, amma ba a gano shi ba. Haka kuma an gano wasu motoci guda hudu duk da cewa har yanzu ana ci gaba da kwalfe kududdufin. Tuni wadansu suka gane motar dan uwansu da ya bace da kuma motar Kamfanin Sufuri na Jihar Gombe kirar bas, amma ba a gano Janar Alkali ba da sauran mutanen da suke cikin motocin.

Abin da ke nan kawai shi ne, dama tuntuni miyagun mutanen da ke wannan garin suna tare matafiya a kan hanyar Abuja zuwa Bauchi, su kashe su sannan su jefa motocinsu cikin kududddufin a matsayin ramuwar gayya na harin da ake kaiwa a wasu garuruwan makwabtansu. Ba mamaki an dade ana wannan mummunar aika-aika ba tare da sanin dattawan garin ba da ma watakila da yawa daga cikin mutanen garin. Amma lallai matasan da suke wannan mummunan aikin suna da goyon bayan wadansu daga cikin mutanen garin da ma wadansu dattawan. Don haka muna tare da sojoji dari bisa dari a wannan aiki na binciko Janar din tare da kama duk wanda ke da hannu a lamarin.

Mun ji dadin yadda sojojin suka shiga garin na Du cikin mutunci ba kamar yadda suka taba shiga garin Odi ba a Jihar Bayelsa da Zaki Biyam a Jihar Binuwai. Takardar bore ta rainin hankali da mutane Berom suka tura zuwa ga Babban Hafsan Tsaron Kasar nan bai kamata a saurare su ba. Kamata ya yi ma a bincika duk wanda ya sanya hannu a takardar  domin watakila suna da hannu a lamarin. Ya kumata su ji kunyar abin da suka aikata bisa kokarinsu na yin rufa-rufa a kan wannan aika-aikar.

Sannan kuma muna yin Allah wadai da dukan kashe-kashen da ake yi a Jihar Filato da kasa baki daya, sannan muna kira ga gwamnati da jami’an tsaro su yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen wadannan kashe-kashe a ko’ina.

Bayan haka, tunda an gano akwai masu yi wa mutane kisar gilla a garin Du, dole a kama masu aikata wannan laifi kuma su fuskanci hukunci mai tsanani. Ta yiwu yin hakan ya zama  darasi ga wadanda suke da niyyar fara tare mutane a kan babbar hanya su kashe su.