Kujerar dan majalisa: Ban gamsu da nasarar NNPP ba, zan tafi kotu – Dan Ganduje
Tuni dai ya tafi kotu don neman bin ba’asi
Umar Abdullahi Ganduje, dan Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ya tsaya takarar dan Majalisar Wakilai a jam’iyyar APC, ya ce bai yarda da sakamakon zaben da ya ba NNPP nasara ba.
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai ta ayyana Injiniya Tijjani Abdulkadir Jobe a matsayin wanda ya lashe kujerar dan majalisar a mazabar Dawakin Tofa/Tofa/Rimin Gado, a jam’iyyar NNPP.
- Bukukuwan Easter: Gwamnati ta ayyana Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutu
- Kotun Kano ta umarci magidanci ya yanka zakaransa
Tuni dai Umar, wanda aka fi sani da Abba Ganduje ya maka Tijjani Jobe a gaban kotun sauraron kararrakin zabe.
Abba, ta bakin lauyansa, Barista A.T Falola, ya kuma kalubalanci INEC kan ayyana Jobe a matsayin dan takarar da ya samu rinjayen kuri’un da aka kada a lokacin zaben.
Da ya ke gabatar da kara a gaban kotun, Falola ya roki kotun da ta gudanar da shari’ar a kan Jobe da kuma jam’iyarsa ta NNPP mai sakatariya a unguwar Sharada a Kano