Kujerar Shugaban Kasa ba ta gado ba ce – Shaguben Fayemi ga Tinubu
Ya ce Dimokuradiyya ta ba kowa ’yancin fitowa takarar
Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce kujerar Shugaban Kasa ba ta gado ba ce kuma bai ci amanar tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu ba saboda fitowa takara.
Fayemi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawarsa cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels ranar Laraba.
- An ba maniyyata kwana 7 su gama biyan kudin kujerar Hajji
- An kama shi yana sayar da garin katako a matsayin maganin gargajiya
Gwamnan na Ekiti ya ce yana da kyakkyawar alaka da Tinubun tun zamanin da aka kafa kungiyar NADECO.
Ya ce, “Tinubun da na sani mutum ne da ya yi amanna da dimokuradiyya. Ya yarda siyasa batu ne na ra’ayi, kuma ya kamata mutane su jarraba sa’arsu. Dama haka ya kamata.
“Abin da ake bukata shi ne a kyale kowa ya jarraba sa’ar shi, a bar ’yan Najeriya kuma su zabi abin da suke so.
“Ban yarda a rika amfani da haka wajen nuna yatsa ga wasu ba, kuma na tabbatar Tinubu ba zai yarda da hakan ba.
“Wannan fa kujerar ba ta gado ba ce; batu ake yi a kan Najeriya da kuma ’yan Najeriya.
“Ina da kyakkyawar alaka da Tinubu. Na taba zuwa na ziyarce shi lokacin da yake neman mafaka a shekarar 1994, lokacin da ya fito bayan soke zaben 12 ga watan Yunin 1993 da kuma kafa kungiyar NADECO.
“Tun lokacin muke da kyakkyawar fahimta da mutuntaka a tsakaninmu. Tun lokacin muka fara mu’amala da shi a siyasance kuma dangantakarmu ta kasance mai kyau,” inji shi.
Tuni dai Tinubu da Fayemi suka sayi fom din neman takarar Shugaban Kasa a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.