Kujerar takarar sanatan Kwankwaso tana kasa tana dabo

An samu rudani wajen mika sunan Gwamnan Kano, Rabi’u Musa wankwaso a matsayin dan takarar shiga majalisar dattijai, mai wakiltar Kano ta tsakiya, inda aka mika sunan Kwamishinansa na ayyuyka, Alhaji Abba Yusuf ga hukumar zabe ta INEC. Don haka wannan takarar sanata tana kasa, tana dabo.Gwamnan Kano ya amince ya yi takarar sanata bayan […]

Kujerar takarar sanatan Kwankwaso tana kasa tana dabo
Kujerar takarar sanatan Kwankwaso tana kasa tana dabo

An samu rudani wajen mika sunan Gwamnan Kano, Rabi’u Musa wankwaso a matsayin dan takarar shiga majalisar dattijai, mai wakiltar Kano ta tsakiya, inda aka mika sunan Kwamishinansa na ayyuyka, Alhaji Abba Yusuf ga hukumar zabe ta INEC. Don haka wannan takarar sanata tana kasa, tana dabo.
Gwamnan Kano ya amince ya yi takarar sanata bayan da ya fadi a zaben fitar da gwani na dan takarar shuigaba kasa, a jam’iyyar APC, duk cewa tuni Alhaji Yusuf Abba ya janye wa kwankwaso takarar, amma sia ga shi an haifar da rudani, inda aka ki mika wa Hukumar INEC sunan Kwankwaso, aka sanya na kwmaishinan ayyuka.
Da manema labarai suka tuntubi Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Alhaji Haruna Umar Doguwa kan wannan rudanin sunayen ’yan takarar, sai ya ce, a halin yanzu dai Abba Yusuf ne dan takarar mu a Kano ta tsakiya ba kwankwaso ba.
“Abba Yusuf sji ne dan takarar mu a Kano ta tsakiya, ba Kwankwaso ba. Mun yi hakan ne don cika ka’idojin da Hukumar Zabe ta shimfida game da suaya dan takara. Za a iya janye sunan dan takara bayan an aika da shi, sannan an kayyade wasu kwanaki da za a iya yin hakan, don haka muka aika da sunan Abba Yusuf,” a cewar Alhaji Haruna Umar Doguwa.
Sai dai jiga-jigan jam’iyyar sun nuna matukar mamakinsu kan yadda aka haifar da wnanan rudani na takarar sanatan Kwankwaso a Kano ta Tsakiya.
“Mun cika da mamaki ganin yadda jam’iyya ta mika sunan kwamishinan ayyuka, ba na Kwankwaso ba,” inji wani jigo na jam’iyyar ta APC.
Da aka tuntubi Haruna Doguwa game da janye sunan game da janyewar Abba Yusuf daga takara, sai ya ce, muna sane d ahakan, amma mu mun aiwatar da abin da doka ta tanada. Kuma ya yi saurin janye kansa daga takarar, tun da akwai kwanakin eda donka ta tanada don yin haka.
Shi kuwa Jami’in yada labarai na Gwamna, Malam Halilu dantiye, cewa ya yi, ba shi da masaniyar an maye sunan gwmanan da na wani.
“Ba ni da masaniyar cewa an sauya sunan Mai girma Gwamna da na wani. Abin da kawai na sani, shi ne, Gwamna Kwanbkwaso ne dan takarar sanata a Kano ta tsakiya,” inji shi.