Kukan al’ummar Tsagem ga Gwamna Masari

  Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji aminu Bello Masari ina son isar da sakon mutanen Tsagem ta karamar Hukumar Mani a kan bukatarsu na a shimfixa musu hanya zuwa garin Tsagem daga Muduru. Shi dai wannan gari tsohon gari ne mai daxaxxen tarihi, wanda aka kafa tun Jihadin Shehu Usman Xanfodiyo. An raba romon […]

Kukan al’ummar Tsagem ga Gwamna Masari
Kukan al’ummar Tsagem ga Gwamna Masari

 

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji aminu Bello Masari ina son isar da sakon mutanen Tsagem ta karamar Hukumar Mani a kan bukatarsu na a shimfixa musu hanya zuwa garin Tsagem daga Muduru. Shi dai wannan gari tsohon gari ne mai daxaxxen tarihi, wanda aka kafa tun Jihadin Shehu Usman Xanfodiyo. An raba romon dimaokuraxiyya a lunguna da sakuna Jihar Katsina tun wajen shekarar 1999, kama daga hanyoyi da ruwan sha da asibitoci da sauransu, amma wannan gari kamar an mance da shi. Kwannan nan ne aka haxa wutar lantarki da ta shiga garin, bayan an daxe ana kai ruwa rana, kuma mazauna wannan gari akasarinsu manoma ne da ’yan kasuwa da ma’aikata gwamanati, waxanda suka dogara da waxannan sana’o’i domin dogaro da kansu.

Sai dai abin ban haushi shi ne, wannan gari na fama da matsalar rashin hanya mai kyau, ko ba komai domin kai kayansu kasuwani lokacin damina da rani. Babbar matsalar garin shi ne in lokacin da damina ta yi ba ka iya shigarsa ta hanyar Muduru sai dai ka koma ta Mani ka yo zagaye, saboda akwai wasu koramu da suka ratsa hanyar, waxannan koramu su ne: Kirau da Tuga da wadda ake cewa Jajjas.

Abin da kawai ake bukata shi ne yin manyan gadoji a hanyar waxanda za su taimaka wa ruwa ya wuce ta kasansu. Mutanen garin Tsagem sun daxe suna rokon gwamnatocin da suka wuce a baya a gyara wannan hanyar abin ya ci tura duk da dai hanyar da ma ta Burji ce, amma ba wani kokari da aka yi ko na yi mata malale.

Ya mai girma gwamna muna rokonka da ka dubi mutanen wannan gari a irin adalcinka da kuma kokorin wannan gwamnati taka ta al’umma ka sa a shimfixa mana kwalta zuwa garin Tsagem daga Muduru, ka sa ta a cikin hanyoyinka da gwamnatinka za ta gyara a kasafin kuxi na shekara ta 2018. Ba hanya kaxai ce matsalar garin ba ya mai girma gwamna, mutanen wannan gari na fama da rashin ingantacce kuma wadataccen ruwan sha, domin har yanzu ruwan koramu ne ake sha a garin. Magana ta kusan karshe ita ce da akwai makarantar al’umma ta garin wato ‘Community Arabic Junior Secondary School,’ wadda ake ta faxi tashi ganin ta zauna da kanta, shi ma akwai bukatar gwamnatin da ta shigo ciki ta taimaka ta kara azuzuwa da kuma wadata makarantar da kayan aiki da karin malamai  domin samun cigaba da koyo da koyarwa ga xaliban da ke garin.

A karshe na ke rokonka ya mai girma gwamna ka dubi wannan bukata tamu da idon basira, kuma in da hali ka je ka ga gane wa idanuwanka halin da mutanen garin ke ciki, kila ta haka za a inganta rayuwar mutanen garin domin tafiya da zamani.

Aminu Ahmad Tsagem Marubuci kuma memba na Kungiya marubuta ta kasa (ANA) 08065032730.