Kukan imani

Wani Bafulatani ne ya je Makkah, yana cikin dawafi sai ya ga wasu Larabawa su ma suna yi kuma suna ta yin kukan zubar da hawaye. Ya tambayi cewa: “Su kuma wadannan kukan me suke yi, ko jikkar kudinsu ce ta kata?” Jagoransu ya shaida masa cewa, kukan da suke yi saboda karfin imaninsu ne, […]

Kukan imani
Kukan imani

Wani Bafulatani ne ya je Makkah, yana cikin dawafi sai ya ga wasu Larabawa su ma suna yi kuma suna ta yin kukan zubar da hawaye. Ya tambayi cewa: “Su kuma wadannan kukan me suke yi, ko jikkar kudinsu ce ta kata?” Jagoransu ya shaida masa cewa, kukan da suke yi saboda karfin imaninsu ne, amma ba kudinsu ne suka kata ba. Jin haka sai Bafulatani ya ce: “Mu dai mun gode Alllah, tun da ba mu da imanin da zai sanya mu kuka.”

Daga A. M. Ibrahim