Kukan Kurciya jawabi ne
Gwanayen magana na cewa wanda duk ya samu rana sai ya yi shanya, kuma irin wannan al’amarin ne ya sa tsohon shugaban kasa, Cif Goodluck Jonathan samun bakin magana, wanda a ranar Alhamis xin makon jiya ya wage shi, har ya furta wasu kalamun da suka nuna cewa shi da ‘yan jam’iyyarsa ta adawa, watau […]
Gwanayen magana na cewa wanda duk ya samu rana sai ya yi shanya, kuma irin wannan al’amarin ne ya sa tsohon shugaban kasa, Cif Goodluck Jonathan samun bakin magana, wanda a ranar Alhamis xin makon jiya ya wage shi, har ya furta wasu kalamun da suka nuna cewa shi da ‘yan jam’iyyarsa ta adawa, watau PDP sun ga wallen jam’iyyar APC da kuma gwamnatin da ta kafa. Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta yi wata rawar-a-zo-a-gani ba wajen cika alkawurran da ta xauka yayin da take yakin neman zabe a shekarar 2015.
A matsayinsa na wani jigo a jam’iyyar adawa, tsohon Shugaba Joinathan ya ce maimakon gwamnatin jam’iyyar APC ta tabuka wajen ba mara xa kunya sai kawai aka ga ta shantake, hasali ma ta kasa inganta halin rayuwar talakawan kasar nan. A maimakon haka sai ma ta kara jefa su cikin mawuyacin yanayin da ya kai su ga tagayyara cikin bakar fatara da matsananciyar ukubar rayuwa. A cewarsa ba wani abu ne ba kuwa ya janyo haka illa manufofi marasa kan-gado na tallafar arzikin kasa da gwamnatin APC ta bullo da su.
Tsohon shugaba Jonathan na yin irin waxannan furuce-furucen ne kuwa a daidai lokacin da jam’iyyarsa ta PDP ke kokarin murmurewa daga kayen da jam’iyyar APC ta yi mata a shekar 2015, abin da ko a mafarki ba ta taba zaton zai faru ba, ganin yadda ake kwarzanta ta a matsayin jam’iyya mafi girma da kuma kasaita a nahiyar Afrika. Gwamnatin jam’iyyar PDP, kuma ta yi shekaru goma sha shida tana ta jan zarenta bai tsinke ba, har sai lokacin da talakawan Najeriya suka nuna mata iyakarta, suka ingije ta daga karagar mulki duk kuwa da makudan kuxaxen talakawa da ta yi amfani da su a haramce wajen yakin neman xorewa bisa mulki.
Tsohon Shugaba Goodluck dai bai mance da haka ba, ya kuma ce a yanzu ga shi nan talakawa na nuna cewa ba su ji daxin bana ba tun da dai suna ta tuna bara, musamman ma ganin cewa abin da suke tsammani sun gujewa ne yake bibiye da su har yanzu, kuma bisa ga dukkan alamu da wuya su iya ban-kwana da su kafin zaben 2019. Ya kawo misalin yadda aka yi ta zolayar gwamnatinsa game da manufofinta kan farashin man fetur, amma sai ga shi nan wai bayan fiye da shekaru biyu game da haka babu wani canjin da aka samu illa ma karin farashi aka yi, abin da ya kara jefa kasar cikin matsalolin tattalin arziki da aka kasa shawo kansu balle kuma a magance kwata-kwata.
Baicin haka nan kuma Goodluck Jonathan ya ragargaji Gwamnatin Buhari sosai sa’ilin da ya ce ta kasa magance matsalolin wutar lantarki, abin da jam’iyyar APC ta yi ta kuka da gwamnatinsa, ta kuma yi alkawarin magancewa, kafin kiftawa da bisimilla, da zarar ta kafa gwamnati. Wannan babban alkawari ne da jam’iyyar APC ta kasa cikawa sa’annan rashin wadatacciya, kuma ingantacciyar wutar lantarki, ya janyo sanadiyyar rurrufe masana’antu masu yawan gaske a jihohi da yawa na kasar nan.
To amma idan baki ya san abin da zai faxa bai san amsar da za a mayar ba. Gwamnatin jam’iyyar APC ba ta xauki waxancan zarge-zargen da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi mata sakwa-sakwa ba, domin kuwa Shugaba Buhari ne da kansa ya mayar mar da martani ta bakin babban mai taimaka masa a harkokin yaxa labarai da kuma hulxa da jama’a, Femi Adesina. Ya ce waxancan zarge-zarge duk shirbici ne da soki-burutsu marasa tushe balle makama. Adesina ya ce ai ko da Shugaba Buhari ya yi karin farashin mai daga Naira tamanin da bakwai zuwa Naira xari da arba’in da huxu ‘yan Najeriya ba su tayar da kayar baya ba, sun hakura domin sun amince Shugaba Buhari ba zai yi abin da zai buwaye su ba, ba kamar a zamaninsa ba sa’ilin da talakawa suka yi boren da ya tayar da kasar tsaye a shekarar 2012 bayan ya kara farashin man fetur daga Naira sittin da biyar zuwa Naira xari da arba’in da xaya, hakan kuma ya tilasta shi rage wa zuwa Naira tamanin da bakwai.
To amma idan ‘yan Njeriya a wancan lokacin sun amince da karin farashin man fetur da gwamnatin APC ta yi ido rufe domin sun amince da dukkan abubuwan da Shugaba Buhari ya aiwatar. Ai a halin yanzu ba wanda zai ce bai ji-a-jika, domin wahalhalun tattalin arzikin da ake fama da su a wannan marrar duk sun biyo bayan wancan karin da aka yi ne, sa’annan kuma ga shi nan ana iya cewa ba a ga takamammen fa’idar da aka samu ba daga kuxin karin da aka yi, ba kamar yadda kowa ya gani a kas ba, yayin da marigayi Janar Sani Abacha ya kafa hukumar rarar mai ta PTF a karshin Janar Muhamadu Buihari, wacce ta sarrafa rarar farshin man fetur na Naira biyar kan kowane lita, aka kuma yi ayyukan alheri da yawa da su, waxanda suka amfani jama’a aka kuma ciyar da kasar gaba.
A bisa gaskiya waxancan zarge-zarge na Shugaba Jonathan na da kanshin gaskiya, kuma wajibi ne a dube su da idanuwan basira domin yin gyararrakin da suka kamata, tun da an ce idan ba rami me ya kawo batun rami? Kada batun siyasa ya shiga cikin al’amarin har a kai ga batan basira, domin kuwa an ce daga kin gaskiya sai bata.
Akwai miliyoyin ‘yan Najeriya da ke da rrin wancan ra’ayin na tsohon Shugaba Goodluck Jonathan cewa jam’iyyar APC ce ke mulkin kasar nan fiye da shekaru biyu da rabi, amma suna zargin cewa ba ta kulla komai ba. Akawi kuma wasu miliyoyin talakawa da ke ganin cewa inda jam’iyyar APC ta fi gwanancewa, a tarayya da kuma jihohi, shi ne fannin farfaganda, inda a kullum ake cika kunnuwan talakawa da sambatu marasa tushe balle makama, ake kuma amfani da ‘yan baranda da ‘yan koren gwamnati wajen kazafi da kuma kirkirar kanzil a tashoshin yaxa labarai da kuma shafukkan jaridun ko a yanar gizo ta wayoyin hannu.
Abin da kawai jam’iyyar APC da gwamnatocinta za su yi domin kare mutuncinsu daga talakawan da ke cewa har yanzu ba ta sake zani ba duk da alkawarin canji da aka yi masu shi ne gaggauta xaukar matakan yin canje-canje a salon mulki da kuma dabarun kyautata wa jama’a. Ana dai iya cewa wannan furuci na tsohon Shugaba Goodluck Jonathan kukan kurciya ne, amma fa sai mai hankali kaxai ne zai iya ganewa.