Kukanmu ga Ministan Abuja
Duk da cewa na yarda da dalilan da suka sanya Ministan Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya bayar na dakatar da ayyukan Hukumar Kula da Filaye da Adana Bayanansu (AGIS), ina ganin zuwa yanzu ya kamata a ce an magance matsaloli da kura-kuran da aka gano a hukumar tare da janye dakatar da ayyukanta. […]
Duk da cewa na yarda da dalilan da suka sanya Ministan Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello ya bayar na dakatar da ayyukan Hukumar Kula da Filaye da Adana Bayanansu (AGIS), ina ganin zuwa yanzu ya kamata a ce an magance matsaloli da kura-kuran da aka gano a hukumar tare da janye dakatar da ayyukanta.
Na fadi haka ne saboda lura da cewa hukumar ce kawai ke iya bayar da takardar mallakar fili na gaskiya ba coge ko zamba. Muna fata zuwa yanzu Ministan ya yi waje da baragurbin ma’aikatan hukumar, wadanda a baya suka lalata harkokin raba filaye suka mayar da harkar ta zama cuwa-cuwa da almundahana.
Sai dai kuma ina fatan Ministan zai karkato da bincikensa zuwa kan jami’an hukumar da ke kananan hukumomin yankin Abuja, akwai bukatar ya kafa wani kwakkwaran kwamitin bincike domin gano irin barnar da suke tafkawa. Domin ’yan damfarar filaye suna hada kai da irin wadannan jami’ai da aka dora wa alhakin rarraba filaye a yankunan kananan hukumomin suna kwace halattattun filayen jama’a suna ba wadansu ko ma kawunansu. Zan iya bayar da misali da yankin da nake wato karamar Hukumar Bwari, inda irin wadancan ma’aikata suke hada baki suna cutar da masu filaye ta hanyar kwace musu suna sayarwa.
Misali yanzu a Kubwa sai mutum ya iske fili daya an ba mutum biyar, saboda mmasu damfara (419) suna hada baki da ma’aikatan kula da filaye na kananan hukumomi. Kuma ko mutum ya kai kuka ga manajan kula da filayen kan irin tabargazar da ake tafkawa a yankin ba ya tabuka komai kan ’yan damfarar. Sannan idan mutum ya tunkari ’yan sanda kan batun sai ya iske kamar ’yan 419 din sun riga sun saye su ne. Domin maimakon ya samu sa’ida sai ya zamo kiri-da-muzu da ’yan sanda za a yi amfani a tabbatar da filin na ’yan damfara ne. Wannan yana neman kawo tashin hankali a lokuta da dama, kuma idan hukumomi ba su dauki mataki ba, lamarin zai iya baci.
Don haka ga fahimtata hanyar magance wannan lamari a dawo da aikin Hukumar AGIS wadda ita ce take iya adana sahihan bayanan filayen da aka bayar ga jama’a a Birnin Tarayya, kuma ta haka za a hana hada mutane da yawa a kan fili daya. Domin koda wani ya yi jabun takarda ba zai iya zuwa hukumar ya sauya ta da ta kwarai ba.
Na biyu ina godiya ga Minista Muhammad Musa Bello kan bayar da ayyukan hanyoyi da ya yi a kwanakin baya a Birnin Tarayya, Abuja, sai dai na ga alamar kamar ba a sanya tamu hanyar ta Mpape zuwa Shere ba. Wannan muhimmiyar hanya tun zamanin Minista Nasir El-Rufa’i aka bayar da ita, amma aka shiru a kanta, sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya ci zabe aka rantsar da shi, sannan aka fara yin wasu ayyukan hanyar daga Dirimi. Wannan hanya tana da muhimmanci domin za ta fito da yankuna da dama tun daga Garejin Tifa zuwa Katampe hada da Kashafa da Jika-Kuci da Shafe da Kabusu da sauransu. Sannan a duba aikin wutar lantarki da ya zarce zuwa Shere, shi ma an dakatar da shi shekara-da-shekaru. Wannan gwamnati ta canji mun zabe ta ne domin mu samar da bambanci da gwamnatocin da suka gabata na fada ba cikawa, don haka muna fata Minista zai gaggauta waiwayo wannan yanki namu domin share mana hawaye.
Sannan muna rokon Minista Muhammad Musa Bello ya tallafa wa garin Mpape da taransfomomin wutar lantarki, domin wadanda muke da su sun yi wa garin kadan. Garin Mpape shi ne cibiyar kasuwanci mafi girma a karamar Hukumar Bwari, amma kusan tamkar ba a yankin Birnin Tarayya yake ba, duk da kusancinsa da Gundumar Maitama, Abuja.
Muna fata Minista Muhammad Musa Bello zai dube mu da idon rahama ya hanzarta daukar matakan magance wadannan matsaloli da suke addabarmu.
Alhaji Adamu Shuwa Damboa dan kasuwan ne da ke zaune a garin Mpape, Yankin Bwari, Birnin Tarayya, Abuja. 08055945695, 08033515344