Kuku ya fada tukunyar miya ya mutu

Ya shafe shekara takwas yana aikin dafa abinci.

Kuku ya fada tukunyar miya ya mutu

Wata katafariyar tunkunyar miya

Hakkin mallakar hoto: Dreamstime

A yayin da ake shirye-shiryen daurin aure a kasar Iraki, sai wani mummunan abu ya faru bayan da wani mai dafa abinci ya fada a cikin wata katafariyar tukunyar miyar dafa kaji ya rasu sakamakon kuna mai tsanani.

Mai dafa abincin mai suna Issa Isma’il mai shekara 25, yana girka miyar kaji ne don liyafar bikin aure da za a yi a Gundumar Zakho da ke Arewacin Iraki, sai ya zame ya fada a cikin miyar, kamar yadda kafafen yada labarai na Gabas ta Tsakiya suka ruwaito.

Ba sabon abu ba ne amfani da manyan tukwanen girki don gudanar da bukukuwan aure a Gabas ta Tsakiya, wanda yawanci ake samun mahalarta a tsakanin mutum 200 zuwa 600.

Isma’il dai ya kone a bangare uku na jikinsa, inda kashi 70 cikin 100 na jikinsa ya kone. An kai shi wani asibiti a birnin Dohuk da ke kusa domin yi masa jinya.

Sai dai kuma ya rasu bayan kwana biyar a asibitin na Dohu, kamar yadda kafar labarai ta Al-Bawaba ta ruwaito.

A cewar kafar labarai ta Arab News ta Saudiyya, wadansu iyalansa sun zanta da gidan talabijin na Rudaw kai-tsaye, inda suka ce, Isma’il yana da ’ya’ya uku da ya bari mata biyu da dan wata shida.

“Ya shafe shekara takwas yana aikin dafa abinci, inda ya rika dafa abinci a liyafar daurin aure da wuraren jana’iza da bukukuwa daban-daban.

“A cikin shekara biyu da suka gabata yana aiki ne a zauren da ake cin abinci na akalla kudin Iraki Dinar dubu 25 (daidai da Naira dubu 7 da 42) a kowace rana,” inji dan uwansa mai suna Zerban Hosni, yayin wani shirin gidan talabijin na Rudaw.

Rasuwar tasa ta haifar da bacin rai a shafukan sada zumunta.