Kula da fatar jiki ta hanya mai sauki
Fatar jikin ‘ya mace tana daya daga cikin ababen da suke kara mata kyau. Don haka, bai kamata a yi wasa da kowace harka da ta shafi fata ba. Idan fatar mace ta kasance mai sheki a koda yaushe, lallai maigida ba zai yi tunanin kowace ’ya mace ba a ransa illa uwargida. Mun kawo […]
Fatar jikin ‘ya mace tana daya daga cikin ababen da suke kara mata kyau. Don haka, bai kamata a yi wasa da kowace harka da ta shafi fata ba. Idan fatar mace ta kasance mai sheki a koda yaushe, lallai maigida ba zai yi tunanin kowace ’ya mace ba a ransa illa uwargida. Mun kawo muku yadda ake hada ababen gyara fuska da dama domin samun fata mai sheki da laushi.
• Yana da kyau a kullum kafin a kwanta bacci a shafa man kwa-kwa a fuska domin samun fata mai sheki.
• Ana shafa ruwan ‘aloe bera’ a fuska da fatar jiki domin magance kurajen fuska da jiki.
• Zuma tana gyara fatar jiki, a hada zuma da ruwan ‘rose’ sai a rika shafawa idan ana da fata mai gautsi.
• A sami ruwan ‘glycerin’ da rowan ‘rose’ da kuma ruwan lemon tsami a shafa a fata kafin a kwanta bacci.
• Kurkum da ruwan rake na taimakawa sosai wajen sanya fata laushi da kuma sheki.
• A sami karas a nika shi sai a hada da zuma sannan a shafa a fuska a bar shi tsawon mintuna 15 sannan a wanke. Wannan hadin na sanya fata sheki.
• Idan ana son magance tabo a jiki, a sami ruwan lemon tsami da madara da kuma kafur bayan an kwaba sannan sai a rika shafawa a wannan tabo.
• Domin samin kwalliya mai kayatarwa, za a iya samin ruwan kwai a saka a firiji tsawon mintuna 10 sannan a hada da ruwan lemon tsami da nikakken tumatir. Ana shafa wannan hadin na tsawon kwana 20 domin samin fata mai laushi da santsi da kuma sheki.