Kula da kai
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana lafiya. Yaya sanyi? Da fatan ba a sanya iyaye yawan magana. A yau na kawo muku labarin “kula da kai. Labarin ya kunshi yadda wani yaro Fannami ya rasa ransa.A sha karatu lafiya. Akwai wani yaro a Jihar Borno, wadda ya jima da fama da rashin […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe tare da fatan ana lafiya. Yaya sanyi? Da fatan ba a sanya iyaye yawan magana. A yau na kawo muku labarin “kula da kai. Labarin ya kunshi yadda wani yaro Fannami ya rasa ransa.A sha karatu lafiya.
Akwai wani yaro a Jihar Borno, wadda ya jima da fama da rashin hankali irin na ’yan ta‘adda mai suna Fannami. Yana da taurin kai kuma ba ya jin magana. Mahaifiyarsa ta sha yi masa gargadin ya daina zuwa aiken bakin da bai san su waye ba da kuma hana shi yawace-yawacen banza amma ya ki ji. Ran nan ya fito yawo kan wani layi a Maiduguri sai ya hadu da yara suna kwallo. Nan ya biye musu suka cigaba da yin wasa.
Can sai ga wasu mutane sun taho suna ’yan waige-waige da ya nuna da alama ba su da gaskiya. Nan take suka haka rami suka binne wata katuwar leda. Duk da cewa abokan Fannami sun ga abin da ya faru amma babu wanda ya yi karambanin zuwa wajen don ya leka abin da aka binne.
Da mutanen suka gama binne ledar sai suka hau babur suka gudu. Daga nan sauran yaran da suka ga abin da ya faru kowa ya yi ta kansa anna sau Fannami ya dage sai ja je ya ga ko mene ne aka binne. Nan da nan ya yanke shawarar ya je ya hako ledar kuma ya ga mai ke ciki. Jim kadan bayan ya bude ledar ce sai wani abu ya fashe inda nan take ya kone, kuma ya halaka. Ashe abin da aka binne nakiya ce wacce wadansu batagari suke amfani wajen halaka al’umma babu gaira babu dalili. Hakan ta sa Fannami ya rasa ransa saboda rashin jin magana.
Ina fata wannan zai zama darasi ga yara marasa jin magana.
A karshe ina jawo hankalin yara manyan gobe da su kula da kansu a duk inda suke sannan su rika bin shawarar iyayyen su musamman a zamanin nan da muke ciki.