“Kula da Kai”(0)

Assalamu Alaikum Manyan gobe. Gaisuwa ta musamman a gare ku tare da fatan kuna cikin koshin lafiya.  A yau na kawo muku labarin ‘kula da kai’. Labarin ya kunshi yadda Manyan gobe za su kula da kansu koda Mama da Baba ba sa nan. A sha karatu lafiya.Akwai wani yaro ne a wani kauye makarantarsu […]

“Kula da Kai”(0)
“Kula da Kai”(0)

Assalamu Alaikum Manyan gobe. Gaisuwa ta musamman a gare ku tare da fatan kuna cikin koshin lafiya.  A yau na kawo muku labarin ‘kula da kai’. Labarin ya kunshi yadda Manyan gobe za su kula da kansu koda Mama da Baba ba sa nan. A sha karatu lafiya.
Akwai wani yaro ne a wani kauye makarantarsu na da nisa daga gidansu domin sai an tsallake kogi da bishiyoyi kafin a isa makarantar, don haka a kullum sai iyayensa sun hada shi da ’ya’yan makwabta domin kula da shi.
Ga shi lokacin damuna ne sai babban cikin yaran ya ce idan an tashi musamman lokacin ruwa kada wanda ya fita daga ajinsa zai zo ya dauke shi.
Shi ko wannan yaron da ya ga ’yan ajinsu kowa ya fita kawai sai ya shi ma ya fita ya kama hanyarsa ta zuwa gida a lokacin da ake tafka ruwan sama. Nan fa tsautsayi ya ja shi har ya fada cikin ruwa, da kyar da jibin goshi aka samu aka ceto sa.
To Manyan gobe, darasin wannan labari shi ne da yaron ya saurari abin da mahaifinsa suka fada masa da watakila ba zai shiga cikin halin da ya tsinci kansa ba.
Don haka yana da kyau manyan gobe a rika kula da kai ko da iyaye ba sa kusa.
Sai mako na gaba.