Kula da lafiyar yara abin dubawa ne

Lallai ba karamin hangen nesa uwargidan shugaban kasa Hajiya A’ishatu Buhari ta yi ba, na tunanin kaddamar da hadakar masu ruwa da tsaki a kan samar da hanyoyin haihuwar jarirai lafiya, tare da kula da lafiyar kananan yara da samar da abincin da zai gina musu jiki. A gaskiya idan muka duba yadda ake samun […]

Kula da lafiyar yara abin dubawa ne

Lallai ba karamin hangen nesa uwargidan shugaban kasa Hajiya A’ishatu Buhari ta yi ba, na tunanin kaddamar da hadakar masu ruwa da tsaki a kan samar da hanyoyin haihuwar jarirai lafiya, tare da kula da lafiyar kananan yara da samar da abincin da zai gina musu jiki.

A gaskiya idan muka duba yadda ake samun rahotanni da kididdigar alkalumma masu yawan gaske na mutuwar jarirai ko iyayen su a wurin haihuwa abin ya kai lahaula walakuwata. Haka su ma  kananan yara ‘yan dagwai-dagwai kula da lafiyarsu yana fuskantar kalubale, musamman yaran karkara. Uwa uba ga karancin abinci mai gina jiki da lafiyar yaran ke fuskanta. Ganin hakan ne ya sa a ranar Litinin 9 ga watan 10,2017 uwargidan shugaban kasa ta shirya wani gangamin babban taro, wanda ya gayyato daukacin matan gwamnoni da matan shugabannin kananan hukumomin dukkan jahohin kasar nan, tare da jami’ai da malaman lafiya, ciki kuwa har da ministan lafiya da kungiyoyi da gidauniyoyi na gida da na Majalisar dinkin Duniya don a taru a rufa wa wannan kyakkywan kudirin nata baya; watau tabbatar da dukkanin matan kasar nan suna samun damar zuwa cibiyoyin kula da lafiya a duba su da ’yan tayin cikinsu, har zuwa ga haihuwa. Haka suma daukacin kananan yaran kasar nan su rika samun cikakkiyar kulawar malaman lafiya a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, kuma a duk inda suke. Shi ma samar da abinci mai gina jiki ya kasance iyayen yara sun san shi; kuma sun san hanyoyin da za su rika sarrafa shi ga yaran su don inganta lafiyarsu

Duk an yi ittifaki da cewar ba komai ne ya haifar da kalubalen rasa dukkanin wadancan kulawar ga yaran kasar nan ba illa sakacin shugabannin mu (hukumomi) da mu al’ummar wannan kasa. Ba kowa ya yi wannan hasashe ba illa Uwar-gidan shugaban kasa da wasu masana harkar lafiyar kananan yara. Ta ce abin da ya sa ya zama akwai sakacin hukumominmu shi ne, halin ha’ula’i da mafi yawan asibitocin kasar nan suke fuskanta, har ta kai idan dai har kana son ka samu cikakkiyar kulawa, to, sai dai ka tafi asibitin kudi, ga kuma halin ko in kula da wasu jami’an lafiya suke yi wa majinyatansu saboda rashin iya aiki ko rashin samun horo ingantacce da ba sa samu akai-akai. Ganin haka ne ya sa ta yi kira da babbar muraya, ta hada wannan kasaitaccen taro don a taru a cire kitse a wuta.

Haka kuma ta umarci daukacin matan gwamnoni da masu ruwa da tsaki a cikin wannan lokaci da kowa ya rage wasu al’amura da yake a gabansa a jihohinsu don ya samu damar kulawa ga wannan shiri nata, a taru a mayar da hankali kacokan akan wannan lamari na inganta rayuwar kananan yaran kasar nan. 

Ta ce su nemi gudunmawar mazajensu (gwamnoni) da kungiyoyi masu zaman kansu da malaman addini da sarakuna da shugabannin al’umma, don su tallafa musu wajen ganin an ceto rayuwar kananan yaran kasar nan, kuma  wannan shirin ya zama shi ne ginshikin kafuwa da tabbatuwar samun lafiyar yara na dindindin a kasar nan.

Ta ce lallai a samu sababbin hanyoyi na kai asibitoci kusa ga jama’a, musammam ma matan karkara don kowace mace a kasar nan ta samu dama na yin awon dan tayin cikinta dama haihuwa idan ta kama. Harwayau ta ce kowane yaro a kasar nan yana da hakki ya ga likita idan ba ya da lafiya, kuma ya sha magani, ko ya samu kulawa ta musamman akan harkar lafiyarsa. Ita dai fatanta a samarda sababbin hanyoyin kula da lafiyar haihuwar jarirai, kananan yara da kuma ingantaccen abinci mai gina jiki ga dukkanin daukacin yaran kasar nan bai daya.

Haka suma iyaye da daukacin al’ummomi, uwar gidan shugaban kasa ta yi kira a gare su da su kula da lafiyar yaransu, su ba hukumomi goyon-baya. Iyaye mata su rika zuwa asibiti yin awon cikin su tare da yarda da goyon bayan mazajen su, su rika kai yaransu allurar rigakafin shan-inna, su san wanne ne abinci mai gina jiki ga yaransu don su tsare ba su shi, kuma wanne ne jikin yaransu ba ya bukata su kiyaye shi. Wadannan su ne makasudin babban taron da uwargidan shugaban kasa Hajiya Aishatu Buhari ta kira, domin a gudu tare a kuma tsira tare. 

Al’ummar wannan kasar na maraba da wannan kudiri na uwargidan shugaban kasa, kuma za mu yi iya kokarinmu mu ga mun fadakar da jama’armu, mun ba su shawarwari, mun nusar da su alfanun wannan shiri nata don samar da hanyoyin kula da lafiyar kananan yara da kawo karshen mutuwar jarirai a wurin haihuwa da kuma cututtukan da rashin ingantaccen abinci mai gina jiki ke haifarwa.

Ya Allah ka yi mana jagora ka kuma raya mana yaranmu, ka taimaka mana a cikin tarbiya da kula da lafiyarsu amin.

Za a iya samun A’isha Liman a 08029011185