‘Kula da marayu nauyi ne a kan al’umma’

Abin takaici idan ka kalli wasu iyalin sai ka ga suna musguna wa marayun da ke karkashinsu.

‘Kula da marayu nauyi ne a kan al’umma’

Wasu jami’an kwamitin zakka da wakafi da wasu marayu da aka bai wa tàllafi

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah a Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Malam Hamza Ibrahim Na-Kawu ya ce, abin takaici ne yadda wasu mutane ke sakaci da marayun da ke karkashin kulawarsu, inda suke fifita ’ya’yansu a kan na ’yan uwansu. Malam Hamza Na-Kawu ya ce, hakan na janyo musu fushin Ubangiji.

Malamin ya yi wannan jawabi ne a wajen walimar bude sabuwar Makarantar Haddar Alkur’ani Mai girma don marayu da marasa galihu a garin Kafanchan mai suna Madrasatul Khairiyya Li-Tahfizil Kur’an.

“Babban abin takaici idan ka kalli wasu iyalin sai ka ga suna musguna wa marayun da ke karkashinsu tare da dora musu talla, yayin da su kuma ’ya’yansu ke mike kafafu babu takura,” in ji shi.

Sai ya yi kira ga al’ummar Musulmi su tashi tsaye a daidaiku da a kungiyance don taimaka wa marayu da zawarawa marasa gata da sauran marasa galihu a cikin al’umma.

Limamin Masallacin Jumma’a na Fadar Sarkin Jama’a, Sheikh Muhammad Kabir Kassim, wanda Malam Shafi’i Jume ya wakilta ya jawo hankali kan muhimmancin ilimi a rayuwar Musulmi, musamman don kyautata ibada da rayuwa da neman tsira a Kiyama.

Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Jama’a, Mista Tyen Dogara ya bayyana ilimin addini a matsayin tushen kowane ilimi tun kafin zuwan ilimin boko.

Tun farko a jawabin Shugaban Makarantar Malam Muhammad Tahir Shitu wanda aka fi sani da Malam Shagari Shitu ya ce, ya bude makarantar ce kyauta ga marayu marasa galihu sai dai duk da haka akan samu marasa galihun da ba marayu ba da suke zuwa.

“Zuwa nan gaba za mu kira taron kaddamar da neman gudunmawar gina makarantar saboda amfaninta ga al’ummar da muke ciki.

“Burina shi ne taimakon marayu kuma nan gaba ina son samar da ginanniyar makaranta mai dakunan kwanan dalibai.

“A yanzu muna bukatar taimaka wa wadannan yara da abinci danye ko dafaffe,” in ji shi.

Mai martaba Sarkin Jama’a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II wanda Danmadamin Jama’a, Alhaji Aminu Isa Muhammad ya wakilta ya sanya albarka tare da nuna goyon baya, inda ya yi addu’ar nasara da ci gaban al’ummar masarautar gaba daya.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa