Kula da tafin kafa
Kowa na da lokaci irin nasa yanayin fata. Don haka a lokacin da wasu za su yi kaujen tafin kafa daban yake da yadda wasu za su yi na su. Wani a lokacin sanyi yake samun wannan matsalar wani kuma sai zafi ya shigo yake samun kauje. Don haka dole ne a kula da taffuka […]
Kowa na da lokaci irin nasa yanayin fata. Don haka a lokacin da wasu za su yi kaujen tafin kafa daban yake da yadda wasu za su yi na su. Wani a lokacin sanyi yake samun wannan matsalar wani kuma sai zafi ya shigo yake samun kauje. Don haka dole ne a kula da taffuka kafa. Idan ba’a kula tafin kafa yadda ta dace ba kafar za ta fara tsagewa ko kuma fashewa. Mata da dama na mantawa wajen kulawa da kafa a duk sadda suke kwalliya. Me aka yi idan ko’ina ya yi kyau, amma in aka taka mutum sai a ji kafar da kauje ko kuma faso.
Akwai hanyoyi da dama da za a bi don kulawa da tafukan kafarmu kamar haka;
• Za a iya amfani da ‘baking soda’ (ana samunsa a inda ake sayar da kayan hada ket) da man ‘tea tree’ da man lafinta, sannan a zuba a ruwan dumi a gauraya su, sai a tsoma kafa na mintuna ashirin, sannan a dirza da dutsen goge kafa. Yin hakan na rage fitowar kauje da faso a tafin kafa.
• Man lafinta da ‘sea salt’ da ruwan ‘aloe bera’ da man ‘rosemary’ a hada su a ruwa, sannan a tsoma kafa na tsawon mintuna ashirin, sai a dirza kafa har sai kafa ta fita tsaf.
• Bayan haka, sai a busar da kafa ko a goge da tawul. Sannan a shafa man ‘glycerin’ da na lafinta a fatar kafa da tafin kafa. Sai a yanke farce a gyarasu.
• A samu man ‘glycerin’ da gishirin ‘Epdomr’ (ana samunsu a manyan kantuna da ake sayar da kayan kwalliya) da man ‘tee tree’ da kuma man ‘peppermint’ a zuba su a ruwa sannan a jika kafafun na tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin, sai a dauko dutsen goge kafa a dir-dirza. Za a ga canji.
•Shafa man kadanya a bayan an wanke kafa da ruwan dumi, sannan a sanya safa ana kwana da shi. Yin hakan na taimaka wa tafin kafa sosai.
•A kasance a kullum ana goge kafar da dutsen goge kafa, domin samun tafin kafa mai sulbi da laushi.