Kula da tafin kafa a lokacin hunturu

kafa na daya daga cikin abubuwan da ya kamata mu kula da su, domin idan ba a kula da ita ba, hakan na iya sadiyyar a samin kauje ko faso. A rage dadewa a cikin ruwa idan an zo yin wanka. Yana da kyau a rika wanke tafin kafa da ruwan dumi ba tafasasshe ba. […]

Kula da tafin kafa a lokacin hunturu

kafa na daya daga cikin abubuwan da ya kamata mu kula da su, domin idan ba a kula da ita ba, hakan na iya sadiyyar a samin kauje ko faso. A rage dadewa a cikin ruwa idan an zo yin wanka. Yana da kyau a rika wanke tafin kafa da ruwan dumi ba tafasasshe ba. Sannan kuma yana da kyau a rika shafa mai a kafa a duk lokacin da tafin kafar ya gamu da ruwa. Sa’annan a rage sanya takalma wanda iska ba za ta samu shiga kafar ba.
–    A tsoma tafin kafa a ruwan lemun tsami na tsawon mintuna 10. Yin hakan na fitar da matattar fata daga tafin kafa. Sannan a samu dutsen goge kafa a dirza ta.
–    Za a iya hada man tafin kafa idan aka hada man zaitun da ruwan lemun tsami, sai a rika shafawa a inda ta tsage. Ana girgiza wannan hadin kafin a yi amfani da shi a kullum.
–    Ana shafa man basilin a tafin kafa sannan a sanya safa a kullum kafinn a kwanta barci.
–    Kofi ¾ na man kwakwa da ½ na man kadanya na gyara tafin kafa. Idan aka samo su sai a hada su, sannan a narkar da su a wuta. Bayan ya narke sai a shafa a tafin kafa sannan kuma a sanya safa kafin a kwanta barci.
–    Kada a tsoma kafa a ruwa tsalam haka ba tare da an yi wa ruwan wani hadi daga cikin ababen da na lissafa ba.