Kula da tarbiyyar yara (1)
Tarbiyyar yara magana ce mai matukar fadi,sai dai mu yi iya bakin kokarinmu mu ci gaba da neman taimakon Allah. Daga cikin hanyoyin da ya kamata iyaye su bi domin tarbiyyar yara akwai: NasihaYana da matukar muhimmanci iyaye su sani cewa nasiha babbar hanya ce ta tarbiyyar yara.Domin kuwa duk lokacin da uwa ta zaunar […]
Tarbiyyar yara magana ce mai matukar fadi,sai dai mu yi iya bakin kokarinmu mu ci gaba da neman taimakon Allah.
Daga cikin hanyoyin da ya kamata iyaye su bi domin tarbiyyar yara akwai:
Nasiha
Yana da matukar muhimmanci iyaye su sani cewa nasiha babbar hanya ce ta tarbiyyar yara.Domin kuwa duk lokacin da uwa ta zaunar da ‘yarta ko danta ta yi masa nasiha lokacin da ya yi wani laifi to ya fi nutsuwa da daukar abin da muhimmanci.Wani lokaci iyaye sukan rikita ’a’yansu da duka da zagi da fada gaba daya, ku sani,“Saurin fushi shi yake kawo da na sani.” A irin wannan yanayi sai a yi wa yaro mugun rauni ,wani lokaci ma takan kai ga kisa, ko kuma a koya masa zagi da sauri fushi ba tare da an ankara ba,wato”An bata tara goma ba ta gyaru ba”. Domin kuwa duk abin da ake yi wa yaro yana dauke shi ne a kwakwalwarsa.Yana da muhimmanci mutane su fahimci cewa yawan dukan yaro yana taimakawa waje kara kangarar da shi.
Kula da karatun yara
Yawanci iyaye suna da kokarin tura ‘ya’yansu makaranta ne kawai,amma ba su cika damuwa da bin diddigin abin da ake koya musu ba.Yana da kyau a tura yaro makaranta,kuma duk lokacin da ya dawo a duba littattafansa a ga irin abin da ya koya a makarata. Sannan kada a bari ya rika lalata littattafansa yana yaga su ko ya rika saka musu mai da miya da sauransu.Kuma a rika tambayar malamansa irin halinsa a makaranta.Domin kuwa idan aka yi sakaci yaro ya girma bai san muhimmancin makaranta ba,bai iya karatu da rubutu ba, to za a sami matsala wajen tarbiyyarsa. Kuma kada iyaye su ce lallai su za su zaba wa ’ya’yansu fannin da za su karanta,domin idan ba a yi dace ba,“Garin neman kiba sai a samo rama”.
Kada iyaye su rika fada a gaban ‘ya’yansu
Wani abu da ya kamata iyaye su kiyaye shi ne fada a gaban yara.Bai kamata kullum iyaye su zama masu yin musu a tsakaninsu ba tamkar masu muhawara. Duk lokacin da iyaye suka zama suna yin sa-in-sa alhali yaransu suna kallonsu to lallai sun dauko hanyar bata tarbiyyar ‘ya’yansu. Domin kuwa yara ba za su ga girmansu ba.Kuma za su iya rigima a gaban kowa ba za su ji kunya ba domin sun ga mahaifansu suna yi.
Kada a rika nuna bambanci a tsakanin yara
Tabbatar da adalci a tsakanin yara yana da muhimmanci domin kuwa rashinsa zai iya haifar da gaba ba tare da iyaye sun farga ba.Wannan kuwa ba karamar matsala ba ce a lokacin da iyaye suke kokarin tarbiyyar ‘ya’yansu.Saboda haka duk lokacin da yara suka yi fada ,koda yaran makwabta ne kada a bi son zuciya, a saurare su a yi musu fada, mai gaskiya a ba shi gaskiyarsa dayan kuma a nuna masa kuskurensa.Haka nan kada ka yi wa yaro daya kyauta ka hana sauran ‘ya’yanka.Ko kuma ka bai wa wani abu mai yawa ka bai wa wani kadan, yin haka ba dai-dai ba ne.Yaranka za su tsani wanda kake yi wa kyautar watakila har kai.Kuma duk lokacin da gaba ko kiyayya ta kunno kai cikin iyali, tarbiyya kuma sai a hankali.
Girmama mutane
Yana da kyau iyaye su tabbatar ‘ya’yansu suna girmamasu.Sannan su nuna musu girman yayyensu da kannensu da sauran mutanen gida wannan ya hada da masu wanke-wanke da shara da sauransu, “Durkusa wa wada ba gajjiyawa ba ne”. Kada a bari yaro ya rika yi wa yayyensa rashin kunya kuma kada ya saba da cin zalin na kasa da shi.Idan yaro ya tashi da wannan to lallai zai ga girman sauran jama’a.A koya musa gaishe da mutane da taimaka musu, misali idan an ga babba da kaya sai a sa yaro ya karbi kayan ya kai masa gida.Kuma a fahimtar da shi muhimmancin makwabta da girmama baki, ta hanyar nuna masa “Shimfidar fuska ta fi shimfidar tabarma”.
Furuci
Wadansu iyayen ba su damu da kalaman da ‘ya’yansu suke furtawa ba.Idan yaro ya furta magana mara dadi sai iyaye su fashe da dariya maimakon su kwabe shi.Haka nan sukan bar yaro ya rika tsoma baki a lokacin da manya suke magana.Bai kamata a bar yaro a tsakiyar manya ba,balle ma ya rika katsalandan a cikin zancen da ba na sa ba.Yana da kyau a saka wa bakin yaro linzami ta hanyar kwabarsa.Domin kada ya zama irin mutanen nan da ake cewa,“A bakin wawa, a kan ji magana”.Sannan su ma iyaye sukan yi wadansu maganganu barkatai a gaban ‘ya’yansu,don haka a yi hattara.
Za mu ci gaba!