Kula da tashoshi da bututun mai ya lakume Naira biliyan 167 a watanni 13

Wasu takardun gwamnati sun nuna cewa kamfanonin mai na NNPC ya kashe kimanin Naira biliyan 167 don kula da bututun mai da tashoshin mai wato depot a cikin shekara guda.   Gwamnati ta kafa wani kamfani  mai kula da bututun mai wanda atakaice ake kira NPSC daga kamfanin da ke kula da sayar da albarkatun […]

Kula da tashoshi da bututun mai ya lakume Naira biliyan 167 a watanni 13

Wasu takardun gwamnati sun nuna cewa kamfanonin mai na NNPC ya kashe kimanin Naira biliyan 167 don kula da bututun mai da tashoshin mai wato depot a cikin shekara guda.
 
Gwamnati ta kafa wani kamfani  mai kula da bututun mai wanda atakaice ake kira NPSC daga kamfanin da ke kula da sayar da albarkatun mai da dangoginsa mai suna PPMC a shekarar 2016 inda kamfanin NPSC zai rika kula da depo-depo 21 da kuma bututun mai a kasa baki daya.
 
Wani kundi da Aminiya ta gani ya nuna cewa amma har yanzu depo-depo da yawa musamman wadanda suke dazuka ba sa aiki sannan kuma a tsakanin watan Nuwamban shekarar 2016 da Nuwamban shekarar 2017 an kashe kimanin Naira biliyan 167 a kula da depo-depo da killata bututun mai.
 
Kamfanin yana da bututun mai da suka kai na tsawon kilomita dubu takwas don tura danyan mai zuwa matatun mai da dangogin albarkatun mai da iskar gas zuwa depo-depo na kasar nan.
 
Amma halin da depo-depon da bututun suke ciki ya fito karara lokacin da aka samu karancin mai a kasa baki daya daga watan Nuwamban shekarar 2017 zuwa watan Fabarairun shekarar 2018.