Kula da Yara Cikin Ramadan 2

Assalamu Alaykum; barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga cigaban bayani kan hanyoyin da ma’aurata za su yi amfani da su don samar da cikakkiyar kulawa da ingantacciyar tarbiyya ga yaransu a cikin wannan wata mai alfarma na […]

Kula da Yara Cikin Ramadan 2
Kula da Yara Cikin Ramadan 2

Assalamu Alaykum; barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Ga cigaban bayani kan hanyoyin da ma’aurata za su yi amfani da su don samar da cikakkiyar kulawa da ingantacciyar tarbiyya ga yaransu a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
2. Koyar da su sanin dandanon Ramadan: Kamar yadda muka san cin abinci na maganin yunwa da gina gangar jikin dan adam, to haka nan ayyukan ibada ke gina ruhi, su wanke shi ya yi fes ya rika kyalli. Akwai wani zaki na musamman da masu azumi kan ji cikin ruhinsu musamman in na watan Ramadan ne, sai a koyar da yara fahimtar wannan dandano na ruhi da natsuwar zuciya da Ramadan ke kawowa, wannan zai sa su kara fahimtar amfanin yin azumi kuma su kara dagewa wajen yin azumin.
3. Koyar da su Sallah: Watan Ramadan gaba dayansa watan ibada ne; Sallah kuma ta kasance ibada ce mai tsananin girma cikin ibadu; sai dai kuma duk da sanin girman ibadar Sallah, da yawan iyayen wannan zamani suna sakaci game da kiyayeta akan yaransu; ba su cika sa ido, da yin tsayin daka ga yaransu don ganin suna tsaida ita ba. Ramadan wata dama ce ga iyaye su zauna su binciki yanayin Sallar yaransu, su tabbatar suna yinta kamar Yadda Annabi SAW Ya koyar da ita. Inda aka ga sun yi kuskure sai a gyara masu. A koya masu dukkan addu’o’in cikin Sallah da addu’o’in bayan Sallah. A yi kokarin a dabi’antar da su yin nafilolin da ke tare da Sallolin Farilla. A bisu a hankali yau da gobe ana koya masu har abin ya zama jiki a garesu. Kar a runka ganin kamar ai su yarane ba zasu iya ba, in aka daure aka koya masu a hankali sai su rike su har karshen rayuwarsu. Ma’aurata su rika tayar da yaransu duka Sallar kiyamul layli, wanda ya koma barci sai a kyale shi ya yi barcinsa, amma a cigaba da tayar da shi da haka har wata ran ba zai koma barcin ba.
4. Koyar da su Alkur’ani: Watan Ramadan watan Alkur’ani ne kuma ba abu mai kwararas da ruwan imani cikin zuciya irin karutun Alkurani, balle kuma an gauraya shi da zakin azumin watan Ramadan. Mafi dacewar lokaci don gabatar da karatun kurani cikin wannan wata shi ne bayan Sallar Asuba, don haka sai ma’auarata su tsara wannan ta yadda zai kayatar da yara su ji suna son yi kullum ba fashi ko gardama saboda nishadin da ke ciki:
*Kullum a zabi wata Sura wacce kowa ya iya karantawa, sai iyali duka su rika yin kira’arta gaba daya a lokaci daya. misali, ana iya farawa daga juz’in Amma a yo kasa.
*A zabi wata Sura ta Musamman kullum a haddace Aya daya a cikinta, ayi ta maimata wannan Aya har sai kowa ya haddace ta. Misali, ana iya zabar Suratul Mulk mai Ayoyi talatin, in kullum ana Haddace Aya daya zuwa karshen azumi kowa a gidan zai haddace wannan Surah mai albarka cikin yardar Allah.
*Haka kuma ana iya yin musaffar karatun kurani iyali duka, maigida ya fara karanto Ayar farko cikin wata sura ta musamman, daga nan sai uwargida ta karanta mai bi mata, da haka har a sake kewayo har zuwa karshen Sura.
*Sannan Maigida na iya sa gasa tsakanin yaransa, ya basu wata hadda, duk wanda ya riga haddacewa ayi masa wata babbar kyauta wadda zai ji dadinta sosai cikin zuciyarsa.
5. Hanyoyin Nishadantar Da Su: Ma’aurata zasu iya nishadantar da Yaransu cikin ramadan ta wadannan hanyoyin:
Bayan Buda Baki:
*Samfurin nishadantarwa da yafi dacewa a wannan lokaci shine wasannin m bukatar kuzari da yawa; kamar wasannin buya irinsu odiyi-diyo, wasan tsere, wasannin gada, da sauransu.
*Haka kuma Ma’aurata na iya shirya ma diyansu walimar buda baki dan kayatar da su, sai a shirya masu wani abinci na musamman, asa su gayyato abokaninsu da diyan makwabta suyi buda baki tare.
*Alibidin Ramadan: watau shine ma’aurata su gwada ma yaransu mata yadda zasu dafa wani abinci na musamman da kansu, sai su gayyato