Kula da Yara Cikin Ramadan 3
Assalamu Alaykum; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan hanyoyin da ma’aurata zasu yi amfani da su dan samar da cikakkiyar kulawa da ingantacciyar tarbiyya ga yaransu a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan. Da fatan […]
Assalamu Alaykum; barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin. Ga karashen bayani kan hanyoyin da ma’aurata zasu yi amfani da su dan samar da cikakkiyar kulawa da ingantacciyar tarbiyya ga yaransu a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan. Da fatan Allah Yasa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar dasu, amin.
• 6. Koyar Dasu Tsoron Allah: Tsoron Allah wani babban sinadarin more rayuwar duniyane ga mummunai, wanda duk zuciyarsa tayi riko da tsoron Allah to kariyace gareshi daga dukkan musibu da fitintinun rayuwa. Don haka yana da kyau Ma’aurata su dabi’antar da tsoron Allah cikin zuciyoyin yaransu tun suna kanana; ba wani babban jari ko wani gadon da zasu bar masu da ya wuce wannan. Gashi kuma wannan watane da Allah Ya wajabta mana azumi a cikinsa musamman don mu noma, mu gina, kuma mu habaka tsoron Allah cikin zuciyoyinmu, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya fada a Suratul Bakara, Aya ta 183. Don haka Sai ma’aurata su runka yawan labarta ma yaransu siffofin Allah da girman ikonsa da iyawarsa akan komi da gawurtan mulkinsa, da muhimmancin dake cikin biyayya ga dokokin Allah da dagewa wajen yin ibadodin da zasu kusantar da bawa zuwa gareshi. Su siffanta masu Girman azabar Allah da kuma kaskanci da munin azabar wutar jahannama. Haka kuma duk iyayen dake kwadayin cika zuciyar diyansu da tsoron Allah, to sai su dage wajen karantar da su rayuwar Sahabban Manzon Allah SAW da kyawawan dabi’o’insu da jajircewarsu wajen riko da addini.
5. Koyar da su Kwadayin Rahmar Ubangiji: Ramadana watane dake cike da ni’imomi da rahmomi kala daban-daban. Musamman irin wannan da ya zo mana cikin damina, ga albarkun damina ga rahmomin Ramadana. Mafi daukaka daga cikin rahmomin Ubangijinmu itace Aljannar ni’ima da Allah Ya tanadar ga managartan bayinsa. Sai ma’aurata su runka yawan kwadaitar da diyansu tarin ni’imomi marasa iyaka dake cikin Aljannah, ta yadda zasu ji sun zaku su shige ta. Wannan zai kara masu kwarin gwiywar kara bada kaimi wajen dagewa ga yin ayyukan ibada. Ma’aurata su siffanta ma diyansu dalla-dalla yadda Aljanna take, da irin matakai da darajojinta da kyawawan ayyukan da ke sa a shigeta da munanan ayyukan da ke hana a shige ta. Su labarta masu kofar Aljanna mai suna Arrayyan, wacce masu adumine kadai ke shigarta.
6. Koyar da su addu’a: Watan Ramadana watan amsar addu’a ne don haka sai ma’aurata su kara bada kaimi wajen koya ma diyansu addu’a, su dabi’antar masu da yin addu’o’in azkar na safe da marece. Haka kuma, kullum bayan kammala sahur, maimakon a koma barci, ko ayi ta hira ko kallon talabijin, Mafi kyawon abun yi a wannan lokaci shine addu’a domin sulusin karshe na dare lokacine na amsar addu’a. Sai ma’aurata su tsara yadda zai zama abin burgewa ga yara da iyali duka ta yadda kowa zai ji yana sha’awar yin addu’ar. Misali:
• Kullum a zabi wata addu’a ayi ta karantawa ana maimaitawa har sai kowa ya haddace ta; misali ana iya zabar addu’ar zuwa masallaciko addu’ar shiga masallaci.
• Kullum a zabi wanda zai gabatar da wata addu’a yana fadi ana amsawa. A fara daga Maigida har zuwa na karshe daga cikin yara; misali, ana iya zabar addu’o’in dake cikin al’kurani, addu’o’in alkunut, addu’o’in safiya da marece, addu’o’in neman tsari da sauransu.
• A samu addu’o’in kammala karatun kur’ani na Malamai daban-daban, Misali. Shaykh Sudays, Mahir Almua’akil, Fares Abbad, Abubakar Shatri da sauransu, sai kullam a zabi daya a runka kunnawa a rikoda kowa na saurare.
• A sa yara zu zauna cikin sahu su kalli alkibla tare da daga hannuwansu sama, sannan a fara da dan karamin cikinsu a ce ya roki dukkan bukatocinshi wurin Allah a bayyane kowa na saurare ana amsa masa da amin akan kowace addu’a da yayi, da haka har azo kan maigida da uwargida. Za a iya daukar sautin addu’ar kowanne a waya don tuna baya.
• Ma’aurata zasu iya samar da wani littafi, ayi mashi lakabin littafin addu’a, sai a ba kowa ya rubuta addu’o’insa da bukatunsa wurin Allah, yaran da ba zasu iya rubutawa ba a rubuta masu, sai uba ko uwa su runka karantawa sauran yara na cewa amin.
• Gab da ketowar alfijir kuma lokacine na neman gafara wajen Allah, don haka sai iyali duka suyi ta istingifari gabadaya ko daban daban.
Bayan Sallar Asuba kuma lokacin ambaton Allah ne ta hanyar yin tasbihi, tahmidi, tahlili, takbiri da sauran kyawawan addu’o’i na godiya, jinjina, girmamawa da kambamawa ga Ubangiji Madaukakin Sarki, ayi tayi har zuwa lokacin sallar walha sannan a sallaceta.
6. Koyar Da su Sadaka: Yin sadaka da yawan kyauta nasa taushi da malalar farinciki cikin zuciya, ga kuma lada da budewar kofofin arziki daga Allah SWT. Ma’aurata su koyar da diyansu rabuwa da abinda suke so don kwadayin samun lada wajen Allah da karuwar arzikinsu da zahiri da na zuci. Haka kuma musammam don wannan wata, ma’aurata sai suyi asusun Ramadan ta yadda kowa daga cikin yara kullum zai runka saka wani abu a cikin koda zasu runka cirewa daga cikin kudin taransu ne, ranar da ya cika sai a fasa a ba yara su kyautar da shi ga mabukata. Sannan ana iya sa yara su bayar da koda kala daya ne daga suturunsu, sai a hada gabadaya a kyautar dasu ga mabukata ko akai gidan marayu.
Sai mako na gaba in sha Allah, da fatan Allah Yasa mu dace da daren laylatul kadr, kuma Allah Yasa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.