kulafucin iyaye ga ‘ya’ya: Martani
Yau kamar yadda muka saba na bar wannan fili ga makaranta wannan shafi ne da kuma na Intanet domin su tofa albarkacin bakinsu da fatar nasu sharhin zai kara mana sabon haske kan wannan batu. Na gode: Almajirci: Sakacin iyaye ne? Hakika abubuwan da ka yi bayani cikin wannan sharhi naka, wato na wajabcin kyautata […]
Yau kamar yadda muka saba na bar wannan fili ga makaranta wannan shafi ne da kuma na Intanet domin su tofa albarkacin bakinsu da fatar nasu sharhin zai kara mana sabon haske kan wannan batu. Na gode:
Almajirci: Sakacin iyaye ne?
Hakika abubuwan da ka yi bayani cikin wannan sharhi naka, wato na wajabcin kyautata wa ‘ya’ya bisa daidaito, wadanda mutum ya haifa da wadanda ba shi ya haife su ba, na cikin gidajenmu da na makwabtanmu, haka suke a rayuwar al’ummarmu tun dadewa, daga baya ne al’amurra suka rika sauyawa, har suka kai ga lalacewar da ake ciki yanzu.
Hakika ba mu da abin cewa kan wannan yunkuri na Malam sai addu’a, tare da fatar Allah Ya kara budin basirar lalubo irin wadannan matsaloli don nusar da al’umma ga gayarawa.
Amma ni ina da ja kan batun yara almajirai. Addinin Musulunci tare da kyawawan al’adun kowace al’umma sun wajabta hakkin kulawa da daukar nauyin ’ya’ya da ba su ilimi ko kai su inda za su koyi ilimin, tare da daukar duk wata dawainiyarsu a duk inda suke neman ilimin a kan iyayensu. Idan raunana ne, hakkin ’yan uwa makusanta da makwabta ne su taimaka wa iyayen don sauke wannan nauyi da ke kansu, kamar yadda rubutun Malam ke nuni kan haka a dunkule.
Idan haka ne, da wane dalili wasu iyaye ke yarce ’ya’yansu da Allah Ya ba amanarsu, Ya dora musu nauyin duk wata dawainiyarsu, suke tura su manyan garuruwa da birane ba tare da yi musu kowane irin tanadi na abin da za su ci da suturar da za su daura da makwancinsu da kula da lafiyarsu ba, sai dai su rika yawon bara da talla da aikatau da sace-sace ga sauran al’umma? Shin ina natsuwar da za su samu zama su yi karatun Alkur’anin da ake cewa sun zo nema, alhali suna fama da yunwa da kirci? Duk wanda ya danganta wannan da Musulunci, wallahi ya yi kuskure babba.
Don haka a ganina, babu wata hujja ta irin wannan yawon almajirci sai son rai da guje wa hakkokin ’ya’ya da Allah Ya dora wa iyaye da tozarta tarbiyyar kananan yara da sanya su a mummunar turba ta rayuwa, wanda ya wajaba gwamnatoci da daidaikun jama’a su taru don yakar wannan mummunar al’ada mai bata suna Musulunci da darajar Alkur’ani da cin zarafin kananan yara. Tura yara yawon almajirci da ake yi a halin yanzu, ba shi da wani muhalli a addinin Musulunci.
Allah Ya sa mu gane, amin.
Ni ganau ne ba jiyau ba!
Hassan Kaina Daga Abuja
Wato duk lokacin da kai sharhi kan wani al’amarin rayuwa sai na ga ko dai wannan abu ya shafe ni kai- tsaye ko a fakaice. Dangane da sharhinka ‘kulafucin iyaye ga ’ya’ya,’ wannan shi ma kamar yadda ka nuna sai na ga tamkar da ni kake. (Hoton da ke biye da martani) na wani yaro ne da ake ce da shi Yayangida, sojojin Najeriya ne suka mayar da shi maraya da shi da wasu’yan uwansa su uku, dukkansu yara kanana.
Yadda abin ya faru shi ne na je hutu gida a Potiskum da safe sai na ga yaran unguwa kullum na tafiya makaranta, amma sai na ga wannan yaro yana ta gararamba a cikin unguwa! Ba karatun boko da safe, kuma ba na Islamiyya da yamma. Aka yi ’yan kwanaki ina lura da shi, sai na kira shi na tambaye shi mene ne sunansa, ya ce min Yayangida, na ce ina ne gidanku? Ya ce min gidan su BOMBOY, Bomboy din abokina ne tun muna yara! Na ce kai dan wane ne a gidan, ya ce dan Jummai. Na ce wane ne babanka? Sai ya fashe da kuka! Daga bisani sai ga kanena ya zo, shi ne yake min bayanin sojoji ne suka bindige mahaifinsa a irin abin nan da suke kira harbin da ya shafi wanda bai da laifi a lokacin da suke yaki da ’yan Boko Haram.
Bayan bincike na samu yaron nan cikin ukubar rayuwa, hatta Naira 50 din Laraba na Islamiyya ba wanda zai biya masa, balle kuma na makarantar firamare. Wannan ya sa na sa aka kira min mahaifiyarsa, wadda makwabta muke da su, ta yi min cikakken bayanin yadda abubuwa suka kasance, ta ce a halin yanzu su hudu ne marayu da take kula da su. Da na tambaye ta yadda take samun wannan dama ta ce min, tana wanke-wanke ne a gidan masu kudi tana kula da karatun yayar wannan yaron wadda ke karatun Sakandiren GGSS, Potiskum, kuma ta biya wa kanta ’yan bukatun rayuwa, amma ta ce da ni a gaskiya ba za ta iya daukar dawainiyyar karatun Yayangida da na kanwarsa ba.
Wannan abu ya sosa min rai kwarai da gaske a lokacin da na ga tana zubar da hawaye. Wannan ya sa na dora wa kaina wannan nauyi, a takaice dai yanzu Allah cikin ikonSa Ya nufa na sa Yayangida da kanwarsa makarantar firamare ta dorowa da ke Potiskum, kuma na kudiri aniyar ci gaba da daukar dawainiyarsu akalla zuwa babbar sakandire. In kuma Allah Ya kai ranmu da sukuni zan wuce da su gaba insha Allahu.
Ka san abin da ya sa na yi wannan hobbasa? Abin da ya ja hankalina a nan shi ne kafin na bar Abuja na yi wa ’ya’yana biyu dinki iri bibiyu da wasu ’yan kanti da na hada musu, kana na sanya su cikin mota na kai su wurin shakatawa na Wonderland inda suka hole. Kafin nan sai da na biya kudin makarantar da suke zuwa, amma ga shi na zo gida na ga wani maraya wanda hatta makarantar gwamnati da babu abin zama sai dai aje da sallaya wai ta fi karfin Yayangida!
Shi ya sa na ce sharhinka kamar da ni da irina yake. Ina fata za ka ci gaba da jan hankali da irin wannan cikin rubuce-rubucenka, Allah kuma Ya sa mu dace, amin, summa, amin.