Kulob da dama suna rububi a kan Ramsey
Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna yadda kulob din Chelsea da na Liberpool daga Ingila da kuma na Jubentus da ke Italiya suke rububin dauke dan kwallon kulob din Arsenal Aaron Ramey a watan Janairun 2019. Kamar yadda rahoton da jaridar The Mirror ta Ingila ta kalato ta ce Ramsey dan shekara 27 […]
Rahotannin da ke fitowa daga Ingila sun nuna yadda kulob din Chelsea da na Liberpool daga Ingila da kuma na Jubentus da ke Italiya suke rububin dauke dan kwallon kulob din Arsenal Aaron Ramey a watan Janairun 2019.
Kamar yadda rahoton da jaridar The Mirror ta Ingila ta kalato ta ce Ramsey dan shekara 27 ya shafe shekara 10 yana buga wa Arsenal kwallo, kwantaraginsa da kulob din za ta zo karshe ne a watan Mayun 2019. Sai dai dan kwallon ya ki yarda ya sabunta kwantaraginsa da kulob din al’amarin da ya sa mahukunta kulob din suka shiga cikin damuwa.
A kan haka ne suka yanke shawarar sayar da shi a watan Janairu don kada ya yi musu sakiyar da babu ruwa a watan Mayun 2019.
Sai dai mahukunta Arsenal suna ci gaba da kokarin shawo kansa wajen ganin ya canza shawara don ya sabunta kwantaragin, amma idan ya ki, to duk kulob din da ya yi musu tayi mai kyau, za su cefanar da shi a watan Janairun 2019, kamar yadda wani rahoto ya nuna.
Ramsey yana daga cikin ’yan kwallon da tauraruwarsu ke haskakawa a kulob din Arsenal a bana, inda kawo yanzu kulob din ya lashe wasanni 8 a jere a dukkan wasannin da kulob din ya yi a kakar wasa ta bana, da hakan ta sa kulob din ya koma matsayi na 4 a gasar rukunin firimiyar Ingila a bana.