Kulob din Boca Junior na Ajantina zai gina makarantar wasanni a Katsina
Gwamnatin Katsina tare da hadin gwiwar kungiyar kwallon kafa ta Boca Junior da ke kasar Ajantina za su gina makarantar koyar da wassani a jahar. Daraktan wasanni na jihar Alhaji Nalado Kankiya ne ya shaida haka a ranar Alhamis ta makon jiya a wajen bikin mikawa shugaban makarantar gwamnati ta je-ka-dawo da ke kofar ‘Yandaka da […]

Gwamnatin Katsina tare da hadin gwiwar kungiyar kwallon kafa ta Boca Junior da ke kasar Ajantina za su gina makarantar koyar da wassani a jahar.
Daraktan wasanni na jihar Alhaji Nalado Kankiya ne ya shaida haka a ranar Alhamis ta makon jiya a wajen bikin mikawa shugaban makarantar gwamnati ta je-ka-dawo da ke kofar ‘Yandaka da ke Katsina kayan wassanin guje-guje da tsalle-tsalle wadda kungiyar tsoffin daliban makarantar suka bayar a matsayin gudunmuwa don sake farfado da harkokin wassani a makarantar da aka dauki lokaci ba a yi ba.
Kayayyakin wasannin na dubban Nairori sun hada da rigunan wasa da sandar jifa da kwallaye da sauransu.
Daraktan ya kara da cewa,”kwanan nan Gwamnan Jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema ya bai wa ‘yan wasan kwallon bango da suka yi nasara kyautar Naira milyan biyu tare da filaye ga kowane daga cikin ’yan wasan.
Kazalika ‘yan wasan kulob din Shema ‘yan kasa da shekara 17 tare da takwarorinsu da suka buga kofin zaman lafiya na shugaba Jonaton kowannen su ya samu kyautar fili daga Gwamna Barista Ibrahim Shema”.
Tun farko uban kungiyar kuma tsohon shugaban wannan makaranta Alhaji Haruna dalhatu da yake mika wa daraktan wasannin kayayyakin wasannin a madadin kungiyar tsaffin daliban ya ce,”tsofaffin daliban sun yi la’akari ne da irin yadda harkokin wasanni suka ja baya a makarantar, don haka suke so su zaburar da daliban don ganin an fara wasannin gasa na shekara-shekara a makarantar da aka jima ba a gudanar ba”.
Ya ce makarantar ta yi suna ta fuskar wasanni tun lokacin da Jihgar ke karkashin tsohuwar Jihar Kaduna.
Daga nan ya yi fatan daliban za su sake farfado da wasannin domin tafiya da zamani.
Da yake karbar kayayyakin, shugaban makarantar Alhaji Lado Barau ya yaba wa kungiyar tsofaffin daliban akan irin gudunmuwar da take bai wa makarantar ta fuskoki da dama.
Shugaban ya ce, makarantar ba za ta manta da irin gudunmawar da wasu daga cikin tsofaffin daliban makarantar suka ba su ba. Misali shi ne irin yadda wani tsohon dalibi Injiniya Muttaka Rabe Darma ya gina tare da sanya musu na’urorin kwamfuta. Ya yaba wa kungiyar masu walda ta jiha a kan kokarin da ta yi musu na gyara musu kujeru da tebura kyauta a matsayin tasu gudunmawa.