Kulob din Dolphins yana neman Naira miliyan 106 a kan Ajagun

Kulob din Dolphins da ke Fatakwal wanda ke buga gasar rukuni-rukuni na Najeriya a shekranjiya Laraba ne ya sanya dan wasansa mai suna Abduljaleel Ajagun a kasuwa ga duk wanda yake neman sayensa a harkar wasan kwallo a ciki da wajen kasar nan.Kafar sadarwar MTNfootball.com ta kalato cewa ganin yadda dan kwallon yake tashe a […]

Kulob din Dolphins yana neman Naira miliyan 106 a kan Ajagun
Kulob din Dolphins yana neman Naira miliyan 106 a kan Ajagun

Kulob din Dolphins da ke Fatakwal wanda ke buga gasar rukuni-rukuni na Najeriya a shekranjiya Laraba ne ya sanya dan wasansa mai suna Abduljaleel Ajagun a kasuwa ga duk wanda yake neman sayensa a harkar wasan kwallo a ciki da wajen kasar nan.
Kafar sadarwar MTNfootball.com ta kalato cewa ganin yadda dan kwallon yake tashe a yanzu haka a gasar cin kofin duniya na matasa ’yan kasa da shekara 20 (U-20) da ke gudana a Turkiyya ta sa kungiyoyin kwallon kafa da dama a ciki da wajen Najeriya suka fara rububin dan wasan.
Abduljaleel Ajagun dai shi ne kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Fyling Eagles da ke fafatawa a gasar kuma a wasan farko ya zura kwallaye biyu a ragar Fotugal duk da cewa Fotugal ce ta yi nasara a wasan da ci 3-2.
Haka kuma a wasa na biyu da Najeriya ta yi da Cuba a ranar Litinin da ta gabata, Najeriya ce ta lallasa Cuba da ci 3-0 kuma Ajagun na daga cikin wadanda suka zura kwallayen.
Abduljaleel Ajagun, mai shekara 20, kungiyoyin kwallon kafa da dama ne a Turkiyya da sassan Turai suka nuna sha’awa a kansa da hakan ta sa kulob din Dolphins ya fara tunanin cefanar da shi nan ba da dadewa ba.
“Yanzu haka akwai wani kulob da ke bukatar a sayar masa da Ajagun amma kulob din Dolphins ya nemi ya biya Yuro dubu 500 muddin yana  son ciniki ya kaya”, inji sanarwar da kulob din ya fitar a kafar sadarwarsa a shekaranjiya.
Ko a kwanakin baya kulob din Dolphins ya sayar da daya daga cikin ’yan wasansa mai suna Chidi Osuchukwu ga kulob din Sporting Braga da ke Fotugal a kan Yuro dubu 350 kwatankwacin Naira Miliyan 74 don haka akwai yiwuwar  ya sake sayar da Ajagun ga wani kulob da ke kasar waje.