Kulob din Giwa FC zai buga wasan zakarun Afirka a badi- Koci Tony
Babban Kocin kulob din Giwa FC da ke garin Jos a Jihar Filato Tony Tope Bulus ya bayyana kulob dinsa zai buga gasar zakarun Afirka a badi sakamakon yadda ’yan wasansa suke murza leda gasar Premier ta bana. Koci Tony ya jaddada hakan ne bayan an tashi wasa tsakanin kulob din Giwa FC da kuma […]
Babban Kocin kulob din Giwa FC da ke garin Jos a Jihar Filato Tony Tope Bulus ya bayyana kulob dinsa zai buga gasar zakarun Afirka a badi sakamakon yadda ’yan wasansa suke murza leda gasar Premier ta bana.
Koci Tony ya jaddada hakan ne bayan an tashi wasa tsakanin kulob din Giwa FC da kuma IfeanyiUba FC a filin wasa na Rwang Fam da ke Jos a ranar Asabar da ta gabata.
Kocin ya ce ya gamsu da irin wasan da yaransa suka yi duk da cewa an tafi hutun mako uku a gasar, inda suka buga wasa bisa umarnin da ya ba su har suka samu nasara a kan kulob din IfeanyiUba FC wadanda a baya ake kiransa Gabros International da ci 2-0.
Tony ya ce nasarar da suka samu ba za ta rude su har su manta kalubalen da ke gabansu ba.
“Na ji dadin yadda yarana suka buga wasa. Mun fara wasan da zafi-zafi, inda muka hana abokan karawarmu sakewa. A lokacin hutu mako uku da aka tafi mun yi gyare-gyare, inda a yanzu muka ci ribarsu. Ina da karfin gwiwar za mu buga gasar zakarun Afirka a badi, burina a ce kulob-kulob na kasashen Afrika sun zo buga kwallo a Jos.
“Duk da nasarar da muka samu ba za sa ta mu manta kalubalen da ke gabanmu ba, don haka za mu ci gaba da zage damtse har mu cimma burinmu.” Inji shi.
Shi ma Kocin kulob din Ifeanyi Uba FC, Mitko Dobreb ya yi alwashin samar da kyakkyawan canji a wasan kulob dinsa na gaba.
Mitko mai shekara 60 dan kasar Bulgeriya wanda kulob din Heartland ya kora a shekarar 2009 saboda da zarginsa da yi wa kulob din zagon kasa da kuma nuna miyagun halaye ya yi alkwarin daukaka darajar kulob din IfeanyiUba FC, sannan ya manta da duk wani abu da ya faru da shi a baya.
“Ba mu buga wasa yadda ya kamata ba, mun kasa hana abokan karawarmu rike kwallon, a karshe suka hora mu. Don haka a wasa na gaba za mu sake zubi da tsari na yadda za mu taka wasa.” Inji shi.
Kyaftin din kulob din Giwa FC Charles Heulong ne ya fara jefa kwallo a raga a minti na 23 da fara wasa bayan dan wasan gaba Ibrahim Shua’ibu ya jefa masa doguwar kwallo. dan wasan gaba Edoh Ocheme ya jefa kwallo ta biyu a ragar kulob din garin Nnewi da ke Jihar Anambra a minti na 49 bayan an dawo hutun rabin lokaci.