Kulob din Inter Milan zai yi nadamar sayar da Mateo Kobacicga Madrid – Luis Suarez

dan kwallon gaba a kulob din FC Barcelona da ke Sifen Luis Suarez ya bayyana takaicin ganin yadda tsohon kulob dinsa Inter Milan na Italiya ya sayar da shahararren dan kwallon tsakiyarsa Mateo Kobacic ga kulob din Real Madrid na Sifen.  Ya ce idan kulob din Inter Milan zai tuna, ya taba yin kuskuren  sayar […]

Kulob din Inter Milan zai yi nadamar sayar da Mateo Kobacicga Madrid – Luis Suarez
Kulob din Inter Milan zai yi nadamar sayar da Mateo Kobacicga Madrid – Luis Suarez

dan kwallon gaba a kulob din FC Barcelona da ke Sifen Luis Suarez ya bayyana takaicin ganin yadda tsohon kulob dinsa Inter Milan na Italiya ya sayar da shahararren dan kwallon tsakiyarsa Mateo Kobacic ga kulob din Real Madrid na Sifen.  Ya ce idan kulob din Inter Milan zai tuna, ya taba yin kuskuren  sayar da Andre Pirlo ga AC Milan a shekarar 2001 al’amarin da ya sa kulob din ya koma yana cizon yatsa.  Sai ga shi a yanzu kulob din ya sake tafka kuskuren sayar da dan kwallo Kobacic ga kulob din Real Madrid.
“Ina da yakinin Kobacic dan kimanin shekara 21 da haihuwa zai taka rawar gani a kulob din Inter”, inji Suarez.
Kobacic dai ya koma Madrid ne daga Inter Milan a kan Yuro miliyan 35 kuma kafin karshen wannan mako ake sa ran  zai rattaba hannu a kwantaragin shekaru masu yawa. Mateo Kobacic dai yana buga wasa ne a tsakiyar fili (midfielder).

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram

An tsinci gawar wata mata babu kai a Abuja