Kulob din PSG ya kafa sabon tarihi a Faransa

A farkon makon nan ne kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa ya kafa sabon tarihi bayan ya lashe gasar rukunin kasar da aka fi sani da Ligue 1 ana saura wasanni takwas a kammala gasar.Yin hakan ya sa kulob din ya shafe tarihin da kulob din Lyon ya kafa a shekarar 2007 […]

Kulob din PSG ya kafa sabon tarihi a Faransa
Kulob din PSG ya kafa sabon tarihi a Faransa

A farkon makon nan ne kulob din Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa ya kafa sabon tarihi bayan ya lashe gasar rukunin kasar da aka fi sani da Ligue 1 ana saura wasanni takwas a kammala gasar.
Yin hakan ya sa kulob din ya shafe tarihin da kulob din Lyon ya kafa a shekarar 2007 bayan ya lashe gasar ana saura wasanni biyar a kammala.
Kulob din PSG ya kafa tarihi ne bayan ya lallasa kulob din Troyes da ci 9-0 a ranar Lahadin da ta wuce.
Shahararren dan kwallon  PSG Zlatan Ibrahimobic ne ya zura kwallaye hudu daga cikin tara da suka zura a raga.
Wannan shi ne karo na hudu da PSG take lashe wannan gasa a jere kuma karo na shida a jimulla. Yanzu kulob din ya ba na Monaco da ke biya da shi tazarar maki 25 yayin da saura wasanni 8 a kammala gasar.  Kenan ko da PSG ta rasa sauran wasannin da suka rage mata, kulob din Monaco ba zai iya kamo shi ba.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa