Kumbon China da aka yi harsashen faduwarsa a Abuja ya rikito a Tekun Indiya

Rashin tabbas a kan inda kumbon zai fado dai ya yi ta jefa wasu-wasi da jita-jita iri-iri a sassa da dama na duniya, ciki har da Najeriya.

Kumbon China da aka yi harsashen faduwarsa a Abuja ya rikito a Tekun Indiya

Kumbon China

Daga karshe dai kasar China ta tabbatar da cewa birbishin kumbon da ta harba zuwa sararin samaniya ya rikito a Tekun Indiya yayin da yawancin sassan jikinsa ya gama ci da wuta tun kafin ya rikito.

Rashin tabbas a kan inda kumbon zai fado dai ya yi ta jefa wasu-wasi da jita-jita iri-iri a sassa da dama na duniya.

Ko a ranar Asabar sai da aka yi harsashen cewa akwai yuwuwar birbishin kumbon ya rikito a Babban Birnin Tarayya Abuja ko Beijing na kasar China, ko New York ko Los Angeles a Amurka, ko Madrid a Spain ko kuma a Rio De Janeiro a kasar Brazil.

Ko a shekarar 2020 dai da irin wannan kumbon da ya taba fadowa a kasar Ivory Coast ya yi mummunar barna tare da lalata gine-gine masu tarin yawa.

To sai dai a ranar Lahadi, Hukumar Dake Kula da Sararin Samaniyar Kasar China (CMSA)  a cikin wata sanarwa ta ce kumbon mai dogon zango ya sake dawowa sararin duniya da misalin karfe 10:24 na safe, wato misalin karfe 1:24 na daren ranar Asabar kenan.

Kafafen watsa labaran kasar ta China dai sun rawaito cewa kumbon ya fada ne a kan Tekun Indiya, dab da Tsibirin Maldives.

“Akasarin birbishin kumbon ya kone tun yana sararin samaniya,” inji su.

Kazalika, Sashen Dake Kula da Sararin Samaniya na Rundunar Sojin Amurka shima ya tabbatar da fadowar kumbon a yankin kasashen Larabawa, amma ya ce ba shi da tabbacin ko cikin ruwa ya fada ko kuma kan tandarkin kasa.

China dai ta harba kumbon ne mai tafiyar dogon zango ranar 29 ga watan Afrilu a cibiyar harba makamanta dake Wenchang.

An yi amfani da shi ne wajen harba rukunin farko na na’urorin kasar zuwa matsuguninta na dindindin a karon farko zuwa Duniyar Wata.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC