Kunar Bakin Wake: Zulum Ya Yi Zargin Zagon Kasa

Zulum ya yi kira ga al’ummar Gwoza da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda,

Kunar Bakin Wake: Zulum Ya Yi Zargin Zagon Kasa

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi Allah-wadai da harin bam da aka kai a karamar hukumar Gwoza a matsayin wani zagon kasa ga gwamnatinsa da Kuma shirin sake mayar da ’yan gudun hijirar jihar zuwa garuruwansu na asali.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Maiduguri bayan dawowarsa daga hutun kwanaki 28 da gudanar da aikin Hajjin 2024 da ya yi.

Zulum ya kara bayyana damuwarsa kan lokacin da aka kai harin, wanda ya faru a lokacin da jihar ke bikin ficewar mayakan Boko Haram.

Don haka ya yi kira ga al’ummar Gwoza da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda, yana mai ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta hada kai da ta tarayya don sake tsugunar da ’yan gudun hijira a yankunansu.

A wani labarin kuma, Gwamna Zulum ya jaddada kudirinsa na tallafa wa manoma da magance matsalar karancin abinci a Jihar Borno.

Gwamnan ya yi alkawarin mayar da hankali wajen noma, fadada wuraren da ake nomawa, da kuma tabbatar da karuwar samar da abinci a jihar.

Zulum ya kara da cewa gwamnati za ta samar da iri ga manoma tare da hada hannu da gwamnatin tarayya domin tabbatar da samar da abinci.

Gwamnan ya kuma yaba wa Gwamnatin Tarayya da hukumar alhazai ta kasa kan gudanar da aikin Hajji bana na 2024 cikin sauki, wanda ya bayyana a matsayin wanda ya fi kowannen samun nasara a ’yan shekarun nan.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara