Kuncin Rayuwa: An bukaci jama’a su yawaita tuba ga Allah
An yi kira ga al’ummar Najeriya da su koma ga Allah kana su yawaita tuba zuwa gare su kuma kyautata dabi’un su da ayyukan su. Limamin masallacin ‘yan masara da ke kasuwar Alaba Rago a Legas Shekh Abubakar Muhammad, ne ya yi kiran a sa’ilin hudubar sa ta sallar idin babba a ranar Lahadin da […]
An yi kira ga al’ummar Najeriya da su koma ga Allah kana su yawaita tuba zuwa gare su kuma kyautata dabi’un su da ayyukan su.
Limamin masallacin ‘yan masara da ke kasuwar Alaba Rago a Legas Shekh Abubakar Muhammad, ne ya yi kiran a sa’ilin hudubar sa ta sallar idin babba a ranar Lahadin da ta gabata.
Shaihin malamin ya ce, akwai bukatar al’umma su kara hakuri da halin kunci da ake fama da shi, ya ce rayuwar mummuni a ko wani lokaci riba ce ko halin farin ciki ko aka sin haka, ” Shi mummuni idan Allah ya jarrabe shi da musifa in ya yi hakuri sai ya sami lada hakan ya zame masa kaffara, idan kuma alkhairi ne ya same shi idan ya godewa Allah sai ya kara masa, mafita a wannan yanayi da muka tsinci kanmu a kasa maganin shi addu’a da yawai ta tuba tare da kyautata ayyuka.” in ji shi.
Ya ce, kada idan Allah ya jarabi mutum ya koma gefe guda ya bar jaki yana dukan taiki, ” kada kaje kana zagin wasu ko wani ko kuma zargin wasu akan lalurar da kasami kanka, baka zargin kanka amma kana zargin wasu, wannan ba daidai bane idan mutum ya sami kan sa a wani hali komawa ake ga Allah ayi ta tuba ana neman gafarar sa tare da aiwatar da aikin alheri”