Kuncin Rayuwa: Gwamna Inuwa ya ƙaddamar da rabon tallafin abinci a Gombe
An tsara tallafin ne bayan fahimtar irin ƙalubalen da magidanta ke fuskanta a Jihar Gombe.
A kokarin gwamnatin Jihar Gombe na rage wa talakawa radadin kuncin rayuwa sakamakon janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya ƙaddamar da raba kayan abinci da kayan noma a jihar.
Da yake kaddamar da rabon kayan a garin Dadin Kowa da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa ƙaddamar da rabon kayan tallafin wani gagarumin koƙari ne na tallafawa fiye da mutane 450,000 da za su ci gajiyar sa a ƙananan hukumomi 11 da ke fadin jihar.
- ’Yan sandan Kano sun lallasa ’yan Kannywood a wasan sada zumunta
- Tinubu ya gargadi sojin Nijar kan lafiyar Bazoum
Ya ce a kashin farko da aka ƙaddamar da tallafin, an fara da tallafa wa mutum dubu 30,000 ne, inda kowane mutum zai samu shinkafa mai nauyin Kilo 5 da katon ɗin Taliya 1 da buhunan taki 2 da lita biyu na maganin kashe kwari.
A cewarsa, a wannan karon an sanya kayan noma a cikin rabon kayan abincin saboda shawarar tana da matuƙar tasiri duba da yadda kaso mai tsoka na al’ummar Jihar Gombe suka dogara da noma wajen gudanar da harkokin rayuwarsu.
Gwamna Inuwa ya ce bayar da tallafin noman zai taimaka matuƙa wajen samar da isasshen abinci a lokacin kaka.
Ya ƙara da cewa, an tsara tallafin ne bayan fahimtar irin ƙalubalen da magidanta ke fuskanta a Jihar Gombe sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki.
Ya yi kira ga al’umma masu hannu da shuni da su sanya tausayi a mu’amalar su, tare da tallafa wa mabuƙata.
“Mu tallafa wa maƙwabtanmu, mu ba da taimako ga mabuƙata, mu ci gaba da tallafawa juna ta hanyar haɗin kai.”
Sannan sai ya kirayi jami’an rabon kayayyakin da ƴan sa kai su gudanar da ayyukan su cikin gaskiya da riƙon amana don tabbatar da gaskiya da adalci.
Daga nan sai ya ce baya ga ƙoƙarin rage raɗaɗin da ake ci gaba da yi, ya tabbatarwa jama’a cewa gwamnatin sa tana ƙoƙarin ƙara samar da ayyukan yi ga al’umma don bunƙasar harkokin ci gaba, da daƙile ƙalubalen tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta.
Shi ma Shugaban kwamitin kula da rabon kayan abinci na jiha Abdullahi Haruna Abdullahi, ya tabbatar wa Gwamnan cewa kwamitin zai gudanar da aikin sa cikin tsantseni da tsoron Allah don amfanar al’umma.
Abdullahi wanda kuma shi ne Sakataren Zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe SEMA, ya bayyana cewa an kafa wasu ƙananan kwamitoci a matakin ƙananan hukumomi da gundumomi don tabbatar da cewa kayayyakin sun kai ga marasa galihu a jihar.