Kuncin Rayuwa: A Fara Yin Alkunut —JIBWIS

Shugaban kungiyar Jama’atu a Jihar Gombe, Injiniya Salisu Muhammad Gombe ne ya bada sanarwar hakan

Kuncin Rayuwa: A Fara Yin Alkunut —JIBWIS

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta umurci dukkan masallatanta na Kamsus Salawatna Jihar Gombe da su fara gabatar da Alkunut saboda neman sauki daga tsada da kuncin rayuwa da ake fama da ita.

Shugaban kungiyar Jama’atu a Jihar Gombe, Injiniya Salisu Muhammad Gombe ne ya bada sanarwar hakan.

Ya bayar da umarnin fara Alkunut din ne a taron kungiyar na jiha da ta gabatar da rahoton kwamitin shirya Tafsiri da malamanta suka gabatar a Watan Ramadan.

Shugaban nan take ya bayar da umarni cewa nan take masallatan kungiyar a fadin jihar su fara Alkunut kasancewar rayuwa tamyi tsada jama’a suna cikin kuncin rayuwa.

Don haka ya ce ya kamata a fara gabatar da al’kunuti ko Allah Zai kawo sauki na wannan bala’in da aka samu kai a ciki.

A taron an tattauna ayyukan da kungiyar ta Izala ta tsara gabatarwa na cigaban addini a yankunan kananan hukumomi 11 na Jihar Gombe.

Sannan cikin farin ciki ya karbi rahoton Malaman da suka gabatar da Tafsiran a wurare sama da 60 a jihar, inda  har aka kammala Tafsiran ba a samu wani rahoto marar dadi kan wani Malamin kungiyar Izala ba.

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda