Kuncin rayuwa ne ya sa na shiga sata – Magidanci mai ’ya’ya 6

Ya ce kuncin rayuwar yau da kullum ne ya sa ya shiga harkar

Kuncin rayuwa ne ya sa na shiga sata – Magidanci mai ’ya’ya 6

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wani magidanci da aje zargi da fasa shagunan mutane yana yi musu sata.

Wanda ake zargin ya ce matar sa daya ’ya’ya shida, kuma kuncin rayuwa ne ya jefa shi a yanayin domin ya samu yadda zai ciyar da su.

Da yake gabatar da mutumin ga manema labarai a hedkwatar rundunar Kakakinta, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce wanda ake zargin na cikin wadanda suka addabi jama’a da sata a garin Gombe.

Wanda ake zargi da satar

Da wakilin mu yake tambayar sa don jin abin da ya kai shi ga shiga sata ganin yana da iyali sai ya ce kuncin rayuwa ne, amma duk da haka kuma shi kafinta ne.

A cewarsa, wannan shi ne karon farko da ya fasa shago da sunan sata, kuma daga yanzu hakan ya zamar masa izna.

Ya kara da cewa shaguna biyu ya fasa a unguwar Federal Low Cost kuma kayan da ya sata zai sayar ne don ya sayi abinci.

Kayayyakin da ake zarfin mutumin da sata sun hada da kafi-zabo da madara da makaroni da sabulai da man wanke kai da taliya da kayan shayi da sauran kayan masarufi.

ASP Mahid Abubakar ya ce da zarar sun kammala bincikensu za su tura shi zuwa kotu domin fuskantar shari’a.