Kungiya na qoqarin farfaxo da zaman lafiya a Najeriya
Kungiyar Farfaxo da Zaman lafiya tare da Sasantawa Tsakanin mabambanta addinai ta qasa ta lashi takobin yin duk mai yiyuwa don ganin ta dawo da zaman lafiyar da aka sani tsakanin mabiya addinai daban-daban a qasar nan. Shugaban Qungiyar Pastor Yohanna Y. D Buru ne ya bayyana haka a lokacin da qungiyar ta kai […]
Kungiyar Farfaxo da Zaman lafiya tare da Sasantawa Tsakanin mabambanta addinai ta qasa ta lashi takobin yin duk mai yiyuwa don ganin ta dawo da zaman lafiyar da aka sani tsakanin mabiya addinai daban-daban a qasar nan.
Shugaban Qungiyar Pastor Yohanna Y. D Buru ne ya bayyana haka a lokacin da qungiyar ta kai ziyara ga fadar Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Talatar da ta gabata.
Tunda farko Pastor Yohanna ya bayyana cewa an kafa qungiyar wacce ta qunshi mabiya addinai daban-daban a shekarar 2012 biyo bayan yawan samun tashin rigingimun addini a qasar nan musamamn ma a jihohin Arewacin qasar nan. “Don haka muna qoqari mu ga mun sulhunta tsakanin waxanda rigingimun addini suka rutsa da su don ganin sun yafe wa juna tare da ci gaba da zaman lafiya a tsakaninsu.”
Pastor Yohanna ya qara da cewa “Ada Arewa an san mu a matsayin tsintsiya maxaurinki xaya duk kuwa da bambancin addinin da ke tsakaninmu, amma sai gashi an wayi gari abubuwa na faruwa na ban tsoro a tsakaninmu. Da zarar an samu wani xan savani tskaninmu sai ka ga an fara aukawa juna da kashe-kashe. Muna so mu kawar da wannan a tsakaninmu tare da ganin mun dawo da zaman lafiya a tsakaninmu kamar yadda iyayenmu da kakannimu suka zauna.”
A cewar Pastor Yohanna qungiyarsu ba za ta gajiya ba wajen shiga loko da saqo wajen fahimtar da al’umma muhimmancin zaman lafiya. Da yake mayar da jawabi Mai Martaba Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi na Biyu ya yi kira ga qungiyar da ta qara zage dantse wajen fahimtar da al’umma muhimmancinzaman lafiya. “Kamar yadda ake faxi babu wani addini na gaskiya da yake yin kira ga tashin hankali, don haka babu wani dalili da zai sa Musulmi ko Kirista su riqa tayar da hankulansu. Akwai buqatar mabiya mabambantan addinai su fahimci cewa muna buqatar ci gaban qasar nan, wanda kuma hakan ba zai samu ba sai da cikakaken zaman lafiya.”
A cewar Sarkin savani na addini ko na fahimta ba zai qare ba, amma idan har aka samu kowa ya girmama tare mutunta xan uwansa to za a samu yalwar zaman lafiya da fahimtar juna a tsakani.