Kungiya ta bukaci a gaggauta fara aiki da dokar nakasassu
Kungiyar Fafutikar Samar da Ilimi ga Nakasassu ta Jihar Kano (KANAWA Educational Forum) ta yi kira ga Gwamnatin Jiha ta gaggauta fara amfani da dokar da za ta kula da al’amurar nakasassu wacce Gwamnan Jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya sanya wa hannu a watannin baya. Shugaban Kungiyar Malam Abba Sarki Sharada ne ya yi […]
Kungiyar Fafutikar Samar da Ilimi ga Nakasassu ta Jihar Kano (KANAWA Educational Forum) ta yi kira ga Gwamnatin Jiha ta gaggauta fara amfani da dokar da za ta kula da al’amurar nakasassu wacce Gwamnan Jihar, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya sanya wa hannu a watannin baya.
Shugaban Kungiyar Malam Abba Sarki Sharada ne ya yi wannan kira a lokacin bikin taya murna da kungiyar ta shirya ga daya daga cikin ’ya’yanta Farfesa Jibril Isa Diso wanda Jami’ar Bayero ta ba shi shaidar kaiwa matakin Farfesa a bana.
Da yake bayani kan muhimmancin ilimi ga nakasassu, Shugaban Kungiyar ya yi misali da Farfesa Jibrin Diso ganin cewa, duk da yana da nakasa ta rashin gani amma bai zauna haka ba, inda ya yi ta karatu da bincike duk ba ya gani ga shi yau ya zama Farfesa a jami’a, “Wannan wata allura ce ga nakasassu da sauran masu cikakkiyar lafiya don yin koyi da shi,” inji shi.
A jawabin Farfesa Jibril Isa Diso ya gode wa kungiyar bisa karramarwar da ta yi masa inda ya yi kira ga iyaye su daure su rika tura ’ya’yansu zuwa makaranta don samun ilimi. “Babu shakka ilimi yana da matukar muhimmanci ga rayuwar dan Adam, don Allah Ya yi mutum da wata nakasa ba yana nufin shi ne karshen rayuwarsa ba ke nan. Don haka akwai bukatar iyaye su taimaka wa irin wadanann yara wajen ganin sun samu ingantaccen ilimi domin su guje wa fadawa cikin barace-barace,” inji shi
An haifi Farfesa Jibrin Diso a 1957. Ya samu digiri na farko a bangaren Ilimin Falsafa a Jami’ar Birmingham da ke Birtaniya. Kuma ya sake samun wani digirin na farko da na biyu da na uku a Sashen Nazarin Halayyar Dan Adam a Jami’ar Bayero da ke Kano.