kungiya ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta binciki kamfanonin wutar lantarki
kungiyar Manyan Ma’aikatan Wutar Lantarki da Makamantarts (SSAEAC), ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da binciken kwarewa a duk kamfanonin samar da wutan lantarki domin tabbatar da cewa kamfanonin suna aiki yadda ya kamata.kungiyar ta ce, binciken kwararrun yana da matukar amfani musamman domin a san yanayin karfin kowane kamfani da darajarsa a lokacin da […]
kungiyar Manyan Ma’aikatan Wutar Lantarki da Makamantarts (SSAEAC), ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta gudanar da binciken kwarewa a duk kamfanonin samar da wutan lantarki domin tabbatar da cewa kamfanonin suna aiki yadda ya kamata.
kungiyar ta ce, binciken kwararrun yana da matukar amfani musamman domin a san yanayin karfin kowane kamfani da darajarsa a lokacin da aka karbi ragamar samar da wutar da kuma darajar kamfanin a yanzu.
Shugaban kungiyar, Kwamared Chris Okonkwo wanda ya fadi haka a wata sanarwa ya ce “Ya kamata gwamnati ta gano ko an samu karin karfi kuma wace daraja asuke da ita da kuma a san ko an karkace daga alkawarin da aka yi kafin watan Oktoban shekarar 2013 zuwa yau da kuma sanin karfinsu a kowane lokaci, domin babbu tabbas kan kamfanonin..