Kungiya ta bukaci ICPC da ta binciki Oshiomhole

Wasu kungiya masu gangami a yau Laraba sun halarci hedkwatar Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC da ta gurfanar da shugaban jam’iyyar APC na kasa Adam Oshiomhole. Kungiyar mai suna ‘Coalition for New Nigeria (CNN)’ ta ce suna bukatar a tsare shugaban jam’iyyar saboda matsalolin da ya janyo a […]

Kungiya ta bukaci ICPC da ta binciki Oshiomhole

Adams Oshiomhole

Wasu kungiya masu gangami a yau Laraba sun halarci hedkwatar Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC da ta gurfanar da shugaban jam’iyyar APC na kasa Adam Oshiomhole.

Kungiyar mai suna ‘Coalition for New Nigeria (CNN)’ ta ce suna bukatar a tsare shugaban jam’iyyar saboda matsalolin da ya janyo a cikin jagorancin jam’iyyar.

Wanda ya jagoranci ayarin kungiyar Barista Stanley Onu ya bayyana wa manema labarai cewa, yana shawartar Oshiomhole da ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon tuhumar da hukumar tsaron farin kaya ta DSS take yi masa.