Kungiya ta kai wa kwamishinan ’yan sandan Jihar Yobe ziyarar ban girma
Kungiyar Kare Hakkin Jama’ar Yobe ta Network of Yobe Cibil Society Organizations (NYSCO) a karkashin jagorancin Babban Daraktanta, Alhaji Baba Shehu ta kai ziyara ga Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe, Alhaji Yahaya Sahabu Abubakar. Yayin ziyarar mambobin kungiyar sun shaida wa Kwamishinan bukatar samar da tsarin ’yan sandan al’umma (Community Policing), tare da bukatar a […]
Kungiyar Kare Hakkin Jama’ar Yobe ta Network of Yobe Cibil Society Organizations (NYSCO) a karkashin jagorancin Babban Daraktanta, Alhaji Baba Shehu ta kai ziyara ga Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Yobe, Alhaji Yahaya Sahabu Abubakar.
Yayin ziyarar mambobin kungiyar sun shaida wa Kwamishinan bukatar samar da tsarin ’yan sandan al’umma (Community Policing), tare da bukatar a duba kararrakin da suka jima a kotuna ba a waiwaye su ba da kuma yadda za a kawar da cin zarafin ’ya’ya mata.
Shugaban Kungiyar ya ce, a kullum suna wayar da kan jama’a kan muhimmancin taimaka wa jami’an tsaro; sai dai ya ce jan kafar da ake yi wajen gudanar da bincike kan cin zarafi na jawowa jama’a su fid da rai daga tunanin za a yi musu adalci. Sai suka yi kira ga Kwamishinan kan a rika gaggauta gudanar da bincike kan kararrakin da suke kotuna.
Alhaji Baba Shehu, ya ce kungiyar tana da kwararrun da ake bukata wajen gudanar da irin wannan aiki, sannan ya tabbatar wa Kwamishinan samun cikakken hadin kai da goyon baya daga gare su.
Da yake mayar da jawabi, Alhaji Yahaya Sahabu Abubakar, ya ce ziyarar tasu ita ce irinta ta farko gare shi a kwanakin nan kuma an yi ta a lokacin da ya dace.
Kwamishinan ya yaba wa ’ya’yan kungiyar inda ya ce suna taka rawar gani sosai kuma su abokan aiki ne wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya ce a bangaren kare hakkokin mata da hana cin zarafinsu da yanzu ya zama ruwan dare musamman a garin Potiskum da kuma rikicin manoma da makiyaya, suna aiki ba dare ba rana wajen shawo kan lamuran.
Sai ya hori kungiyar ta yi amfani da kafafen watsa labarai da sauran kafofi domin ilimantarwa da fadakar da jama’a kan matsalolin da suka bayyana masa.
Kwamishinan ya koka kan karancin ’yan sanda a jihar inda ya ce ba su wuce dubu uku da suke kula da jama’a sama miliyan biyu da rabi a jihar.